Jihohi 9 ne masu arziki a Najeriya, 12 matsiyata ne kuma duk Arewa suke - Masanin Tattalin arziki

Jihohi 9 ne masu arziki a Najeriya, 12 matsiyata ne kuma duk Arewa suke - Masanin Tattalin arziki

- Shahrarren masanin tattalin arziki a Najeriya ya kasa jihohin Najeriya kashi uku bisa arzikin da suke da shi

- Bismarck Rewane na daga cikin masu baiwa shugaba Muhammad Buhari shawari kan tattalin arziki

- Yace wajibi ne a samu shugabanni na kwarai muddin ana son gyara

Shugaban kamfanin Financial Derivatives Company Limited (FDC), Mr. Bismarck Rewane, ya bayyana cewa jihohi tara ne kawai a kasar nan masu dan arziki da cigaba.

A cewarsa, wadannan jihohi sune Kwara, Oyo, Osun, Ekiti, Ogun, Ondo, Edo, Lagos da Anambra, Thisday ta ruwaito.

Rewane ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar domin murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka.

Ya ce akwai wasu jihohi 12 da manyan matalauta ne a kasar kuma dukkansu Arewacin Najeriya suke.

Jihohin sune Yobe, Borno, Jigawa, Kano, Bauchi, Gombe, Plateau, Adamawa, Taraba, Sokoto, Zamfara da Niger.

DUBA NAN: PDP ta yi kira ga inganta tsaro a Kaduna: Yan bindiga sun kai wa dan majalisar wakilai farmaki

Jihohi 9 ke masu arziki a Najeriya, 12 matsiyata ne kuma duk Arewa suke - Masanin Tattalin arziki
Hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta rincabe da hayaniya yayinda mambobi 2 suka sauya sheka daga PDP zuwa APC

Hakazalika ya ce sauran jihohin 15 na tsaka-tsaki, talauci bai musu katutu ba kuma ba su da arziki sosai.

Wadannan jihohi sune Katsina, Kebbi, Kaduna, FCT, Nasarawa, Kogi, Benue, Enugu, Delta, Imo, Akwa Ibom, Bayelsa, Rivers da Ebonyi,

A cewarsa, jihar Anambara cewa mafi karancin talakawa da kashi 14.2% yayinda jihar Taraba ce mafi yawan matalauta da makin 39.1%.

Jawabin da Rewane ya gabatar ya nuna cewa irin arziki da rashin arzikin da ke kasar.

Rewane ya bada shawaran cewa wajibi ne a samu shugabanni na kwarai da hukumomi na gaske domin shawo kan matsalan tattalin arzikin da ake ciki.

"Najeriya na bukatar ingiza mai karfi da zai farkar da ita daga bacci saboda ta yaki talaucin da take fama da shi, " Ya kara

A wani labari na daban, shugaban IAZE, Sheikh A. G Mika'il ya sanar da manema labarai a birnin Kebbi yadda 'yan ta'adda suka yi garkuwa da mutane 18 a jihar Kebbi. Ya roki jami'an tsaro da su taimaka su cetosu daga hannun 'yan bindigan. A ranar 25 ga watan Satumbar 2020, 'yan bindiga sun kai hari, inda suka kashe mutum 1 a Akawo, suka kuma kashe mutane 2 a 'Yar Kasuwa. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel