Yanzu yanzu: Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a jihar Zamfara

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a jihar Zamfara

- Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a gundumar Gamji, karamar hukumar Bakura, jihar Zamfara, Sani Dangwaggo

- Kasa da awanni 15 da sace shugaban jam'iyyar, yan bindigar sun tuntubi iyalansa, inda suka bukaci N10m a matsayin kudin fansa

- Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Zamfara, Muhammad Shehu, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a gundumar Gamji, karamar hukumar Bakura, jihar Zamfara, Sani Dangwaggo.

Majiya daga iyalansa sun bayyana cewa an sace Mr Dangwaggo a daren ranar Talata da misalin karfe 11:00 na dare. Yan bindigar sun sace shi a gidansa da ke garin Gamji.

Shehu Isa, sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC na jihar Zamfara, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Premium Times a safiyar ranar Laraba.

KARANTA WANNAN: Alkali ya warare auren shekaru 35 saboda mijin ya gaza biyan sadaki

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a jihar Zamfara
Yanzu yanzu: Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a jihar Zamfara - @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Mr Isa ya ce masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan Gangwaggo, inda suka bukaci N10m a matsayin kudin fansa.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa wanda aka yi garkuwa da shi, wakilin mai gundumar Gamji ne.

KARANTA WANNAN: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartaswa a Abuja

Mr Shehu ya ce tuni aka tura jami'an tsaro domin bin sahun wadanda ake zargin, don tabbatar da ganin an sako Dangwaggo nan ba da jimawa ba.

Lamarin na zuwa ne kasa da wata daya gabanin zaben mazabar karamar hukumar Bakura a majalisar dokokin jihar, da za a gudanar ranar 31 ga watan Oktoba.

Gundumar Gamji, a Bakura, ita ce mahaifar dan takarar jam'iyyar APC a zaben majalisar, Bello Dankande.

A wani labarin, A ƙoƙarin da gwamnati ta ke yi wajen ganin ta magance matsalar tsaro da ƙasa ke fuskanta, rundunar sojin Najeriya ta kawo kayan yaƙi na zamani da sauran kayan yaƙe-yaƙe don gudanar da sumame a kan ƴan-ta'adda.

Shugaban rundunar sojin Najeriya,Tukur Buratai, ne ya bayyana hakan a yayin taron tattaunawa da sukayi a ranar talata a garin Maiduguri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel