Yadda Faisal Maina ya yi gaba da gaba da mutuwa a Abuja

Yadda Faisal Maina ya yi gaba da gaba da mutuwa a Abuja

- Faisal Maina, dan tsohon shugaban hukumar fansho, ya tsallake rijiya da baya

- Faisal ya ce wadanda suka kai mishi hari 'yan sanda ne da motocin su guda 7

- Ya ce 'yan sandan sun saita motarsa da bindigogi, hakan ya matukar bashi mamaki

Faisal Maina, dan tsohon shugaban hukumar fansho, ya ce ya samu nasarar tsallake rijiya da baya. A ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba aka kai mishi hari, da kyar ya sha.

Maina ya ce jami'an tsaro ne suka biyo shi a Gwarimpa, ranar Litinin 5 ga watan Oktoba da karfe 8 na dare. Ya ce sun cika motoci 5 kirar Hilux da wasu kananan motoci 2 sun je zasu kashe shi.

A cewarsa sun saita wa motarsa bindiga. Ya ce sai da 'yan sandan masu sanye da kayan aiki suka bi shi har wani wuri, cikin birnin Abuja tukunna suka juya.

Yayi mamakin dalilin da zai sa wani yayi farautar rayuwarsa, duk da yanzu haka yana da tsayuwa a kotu.

Kamar yadda yace duk da dai bai ji ciwo ba, amma motarsa ta samu matsaloli. Bayan Faisal ya bayyana a kotu wuraren karfe 2 na rana, ya ce faruwar al'amarin ya janyo Lattin da yayi a kotu.

Zaman kotun bai yiwu ba sakamakon rashin zuwan mai shari'a Okon Abang.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda aka saki tsohon shugaban hukumar fansho bayan adana shi a gidan gyaran hali dake Kuje da aka yi na watanni 9.

KU KARANTA: Dalilin da yasa na yi nadamar taya Buhari kamfen a 2015 - Tsoho mai shekaru 80

Yadda Faisal Maina ya yi gaba da gaba da mutuwa a Abuja
Yadda Faisal Maina ya yi gaba da gaba da mutuwa a Abuja. Hoto daga @ChannelsTv
Asali: Twitter

KU KARANTA: 2023: Ka taimakemu kada ka fito takara, za mu iya durkusawa gabanka - Fitaccen jigon Ibo ga Tinubu

A wani labari na daban, kakakin majalisar jihar Edo, Rt. Hon. Frank Abumere Okiye da wasu 'yan majalisar jihar sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba.

Sun bar jam'iyyar adawa ta APC zuwa jam'iyya mai ci ta PDP. Bayan Okiye ya sanar da sauya jam'iyyarsa, ya ce an turo masa wasiku 6 na sauya jam'iyya.

Sun ce sun sauya jam'iyya ne don su nuna yadda suke biye da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel