Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum

Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum

- Gwamnan Borno Babagana Zulum ya shawarci sojoji su rika bin ƴan ta'adda zuwa maɓoyansu ba su rika jira sai sun kawo hari ba

- Zulum ya kuma ce akwai bukatar sojojin su rika gina alaƙa mai kyau da mutanen gari ta yadda za su rika taimaka musu da bayyanan sirri

- Kazalika, ya shawarci a rika nada sojojin da suka dace wurin jagorancin rundunar da ke yaƙi da ƴan ta'adda

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Talata ya lissafa wasu hanyoyi da ya yi imanin idan sojoji sun bi za su iya cin galaba kan Boko Haram.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne wurin taron hadin gwiwa na shugaban sojojin ƙasa na shekarar 2020 da aka yi a Maiduguri a jihar Borno inda shine babban baƙo na musamman.

Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum
Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum. Hoto: @TheGuardianNG
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kamar Ganduje, Gwamna El-Rufai zai yi wa masarautar Zazzau garambawul

A cewarsa rundunar sojojin za ta yi nasara ne kan ƴan ta'addan na Boko Haram idan ta sauya dabarun yaƙin ta.

Ya jijinawa ƙoƙarin sojojin amma duk haka ya ce yana da kyau "mu fada wa juna gaskiya lokutan da muka lura abubuwa suna taɓarɓarewa."

Ya ce gwamnatinsa ba za ta gajiya ba wurin taimakawa sojojin da abinda suke buƙata.

A cikin jawabinsa ya bayyana cewa ya kamata sojojin su rika bin ƴan ta'addan zuwa maɓuyansu suna halaka su ba wai su rika jira sai an kawo musu hari sannan su kare ba.

"Ku dena jira kuna bawa ƴan ta'addan daman su fara kawo harin farko. Tsarin ku ya zama bibiyan duk wasu ƴan ta'addan da suka yi saura bayan kun kai hari."

KU KARANTA: Kishi ya saka ango ya kashe amaryarsa da duka a wurin bikin aurensu a Rasha

Ƴa kara da cewa ya kamata sojojin su gina alaƙa mai kyau da al'ummar yankin.

"Ya zama dole rundunar soji ta gina alaƙa mai kyau da al'ummar garuruwan da suke aiki ta yadda za su rika taimaka musu wurin tona ƴan ta'addan da ke tsakaninsu da masu taimaka musu," in ji shi.

Gwamna Zulum ya kuma yi kira ga Shugaban Sojojin ya duba batun naɗa sojojin da suka Ƙware a matsayin kwamandojin ƴaki da ƴan ta'adda.

Gwamnan ya kuma yi alhinin mutuwar Kwanel Dahiru Baƙo wadda ya mutu makonni da suka gabata yayin wani hari da Boko Haram suka kai.

A wani labarin daban, 'yan bindiga sun kashe jami'in hukumar yaki da masu fasakwabri wato kwastam yayin da ya ke bakin aikinsa a kauyen Dan Arau da ke babban titin Katsina/Jibya.

Sun kashe Garba Nasiru, mai mukamin mataimakin sufritanda ne yayin wani hari mai ban mamaki da suka kai a ranar Juma'a sannan suka tafi da bindigarsa AK 47.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel