Bayan ASUU, NASU da SSANU, malaman makarantun Poly zasu shiga yajin aiki

Bayan ASUU, NASU da SSANU, malaman makarantun Poly zasu shiga yajin aiki

- Da alamun daliban makarantun gaba da sakandare da da sauran hutu a gida bayan hutun cutar Korona

- Yayinda malaman jami'o'i suka lashi takobin ba zasu koma aiki ba, na Poly na barazanan tafiya

- Gwamnatin tarayya ta ce malaman su canza tunani su koma bakin aiki

Manyan ma'aikatan makarantun fasaha a Najeriya watau Poly sun yi barazanar shiga yajin aiki nan da makonni uku idan gwamnatin tarayya ta gaza magance matsalolin da suke fuskanta game da manhajar biya albashi ta IPPIS

Ma'aikatan karkashin kungiyar manyan ma'aikatan makarantun fasaha a Najeriya SSANIP, sun yi ganawar gaggawa a hedkwatar kungiyar kwadago 'Labour House' dake birnin tarayya Abuja.

Sun bayyana rashin amincewarsu da yadda hukumar kula da makarantun fasaha na kasa NBTE ke gudanar da wasu ayyukanta.

DUBA NAN: Hoton Sanata Goje da sabuwar amaryarsa Aminatu Binani ya bayyana

Bayan ASUU, NASU da SSANU, malaman makarantun Poly zasu shiga yajin aiki
Credit
Asali: Getty Images

Shugaban kungiyar, Philip Ogunsipe, ya bayyanawa manema labarai cewa akwai matsaloli daban-daban da suke fuskanta da manhajar IPPIS.

Daga ciki akwai rashin samun mafi karancin albashi, zabge musu kudin da akeyi ba gaira ba dalili, rashin biyan ma'aikatan lafiya kudin hadarin COVID-19, bata lokaci wajen biyan alawus da kuma cire kudin harajin da ya saba hankali.

DUBA NAN: Gwamnatin Zamfara ta samu kwangilar samar da gwal na N5bn - Matawalle

Ogunsipe yace: "Saboda haka, kungiyar na kira ga dukkan hukumomin gwamnati su gaggauta magance wadannan matsalolin da aka lissafo."

"Hakazalika, kungiya na son sanar da cewa inda ba'a magance matsalar IPPIS ba cikin kwanaki 21 daga yau, za ta canza ra'ayinta kan manhajar."

Game da matsalolin da suke fuskanta da hukumar kula da makarantun fasaha na kasa NBTE kuwa malaman sun ce "idan ba'a magance matsalolin nan da kwanaki 21 da wannan takarda ba, za'a shiga yajin aiki."

A bangare guda, karamin ministan ilmin Najeriya, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba, ya yi kira ga ‘yan kungiyar ASUU na malaman jami’a, su shiga harkar noma.

Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana cewa ana bukatar karin manoma, don haka malaman makarantar na iya rabuwa da aji, su koma gona.

Ministan ilmin ya kuma yi bayani game da shirin da gwamnati ta ke yi na bude makarantu, ya ce za a rika yin darusa da rana da nufin rage cunkoso.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel