Hoton Sanata Goje da sabuwar amaryarsa Aminatu Binani ya bayyana
- Sanata Danjuma Goje na jihar Gombe ya angwance da sabuwar amaryarsa Hajiya Aminatu ranar Juma'a
- Daga cikin wadanda suka samu halarta akwai Gwamnoni, Ministoci da manyan jami'an gwamnati
Hoton tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje, da sabuwar amaryarsa, Aminatu Dahiru Binani, ya bayyana kafafen ra'ayi da sada zumunta.
An daura auren Goje da Aminatu ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja.
DUBA NAN: Ku rabu da zaben jihar Ondo, ku zo ku yaki Boko Haram - Zulum ga Sojoji

Asali: Facebook
A ranar Juma'a, mun kawo muku rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje a ranar Juma'a ya kara aure inda ya aura Hajiya Aminatu Dahiru Binani, a kasaitaccen biki da aka yi a babban birnin tarayya, Abuja.
Kasaitaccen bikin ya samu wakilcin shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, Gwamna Inuwa Abdulkadir na jihar Gombe, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ministan sadarwa Dr Isa Pantami, Sanata Gabriel Suswam, Abdullahi Adamu da Abdulmumin Jibrin.
An fara daura auren da karfe 2:45 na yammaci yayin da tsofaffin gwAmanoni, Ministoci, sanatoci da 'yan majalisar wakilai suka samu halarta.
A yayin jawabi a bikin, Gwamnan jihar Gombe, Abdulkadir, ya yi addu'a ga angon da dukkan jam'iyyar APC a jihar.
KU KARANTA: Gwamnatin Zamfara ta samu kwangilar samar da gwal na N5bn - Matawalle
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng