Ku rabu da zaben jihar Ondo, ku zo ku yaki Boko Haram - Zulum ga Sojoji

Ku rabu da zaben jihar Ondo, ku zo ku yaki Boko Haram - Zulum ga Sojoji

- Gwamna Zulum ya sake tabo babban hafsan Sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai

- Zulum ya yi mamakin ta yaya ake kukan rashin isassun Sojoji amma ana tura wasu kare akwatin zabe

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya shawarci Sojoji su rabu da shirin bayar da tsaro a zaben jihar Ondo na ranar Asabar, 10 ga Oktoba, su fuskanci yan ta'addan Boko Haram a Arewa maso gabas.

Zulum ya bayyana hakan ne a taron babban hafsan Sojin Najeriya daya gudana ranar Talata, 6 ga watan Oktoba a Maiduguri, birnin jihar Borno.

Zulum ya ce ya yi mamaki lokacin da Buratai ya ke alfaharin nasarar da Sojoji suka samu wajen bayar da tsaro a zaben gwamnan jihar Edo kuma suna shirin maimaita hakan a zaben jihar Ondo.

"Lokacin da babban hafsan Soji yayi magana da nasarar da suka samu a zaben Edo da kuma shirin na Ondo, abin ya ban tsoro saboda ina son Sojojin Najeriya su mayar da hankali wajen yakin yan ta'adda," Yace.

DUBA: Ku maye gibin kujerun yan majalisar APC jihar Edo - PDP ga INEC

Ku rabu da zaben jihar Ondo, ku zo ku yaki Boko Haram - Zulum ga Sojoji
Credit: @GovBorno
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2021 ranar Alhamis

Zulum ya bukaci Sojojin su fara shiga lungu da sakon yankin domin sabawa da mutane saboda a yarda da su yayinda suke gudanar da ayyukansu.

Ya yi kira ga Sojojin su kutsa inda yan Boko Haram ke boye kuma su rika bibiya bayan kowani hari.

Ya jinjinawa Sojojin bisa namijin kokarin da sukeyi wajen kawar da yan ta'addan. Ya ce wajibi ne ya yabawa Sojoji duk yayinda suka samu nasara kuma ya sokesu lokutan da sukayi kuskure.

Ya bukaci a hukunta masu yiwa kasa zagon kasa cikin Sojoji da masu farin hula.

A bangare guda, Sojojin Najeriya sun tabbatar da rundunar OSS ta samu nasarar kashe 'yan bindiga 4 a Unguwar Doka dake karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina, duk a cikin shirin kawar da 'yan bindiga a arewa maso yamma.

Rundunar ta samu nasarar kubutar da mutane 4 da 'yan bindigan suka yi garkuwa da su 'yan kauyen Giruwa dake karamar hukumar Dandume a jihar.

Daraktan hukumar tsaro Birgediya janar Bernard Onyeuko, ya bayyanar da hakan a wata takarda da ya gabatar a Special Army Super Camp IV dake karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel