2023: Ka taimakemu kada ka fito takara, za mu iya durkusawa gabanka - Fitaccen jigon Ibo ga Tinubu

2023: Ka taimakemu kada ka fito takara, za mu iya durkusawa gabanka - Fitaccen jigon Ibo ga Tinubu

- Wani shugaban Ibo, Chukwuemeka Ezeife, ya roki 'yan Najeriya da su taimaka su ba dan kudu maso gabas a Najeriya damar zama shugaban kasa

- Ezeife yayi wannan rokon ne ranar Litinin, 5 ga watan Oktoban 2020 a Akwa-Ibom, babban birnin jihar Anambra

- Tsohon gwamnan ya lura da cewa dan kudu maso gabas ne kadai bai taba samun damar mulkar Najeriya ba

Chukwuemeka Ezeife, tsohon gwamnan jihar Anambra, ya bayyana cewa dan kudu maso gabas a Najeriya ne kadai ba'a taba ba damar mulki ba, don haka yana rokon 'yan Najeriya da su taimaka a ba Ibo damar mulki a 2023.

Jaridar Vanguard ta ruwaito yadda shugaban Ibon yayi wannan jawabin ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba, a Akwa lokacin da suka yi wani taron bai wa Ibo damar mulki a 2023.

Ezeife ya nuna alhininsa akan yadda dan kudu maso yamma bai taba samun damar mulkin damokaradiyya ba a Najeriya.

Ya roki 'yan sauran yankunan da su bada hadin kai don ganin wannan buri nasu ya cika.

Ezeife ya ce: "Muna amfani da wannan damar don rokon mutane irinsu Alhaji Bola Tinubu da wasu manya na arewa da su sauya tunani akan kudirin mulkin kasar nan."

Sanata Ben Obi, shugaban taron ya roki 'yan kabilar ibo da su hada kai don cimma wannan kudirin nasu.

Ya ce ba'a bawa kowa mulki sai ya nema.

Ya ce dole ne su taru akan magana daya, su dage wajen tabbatar da cewa an ba Ibo damar tsayawa takarar shugabancin kasa.

Tsohuwar ministar harkokin mata, Josephine Aninah ta ce duk wanda ya nuna takaicinsa akan wannan kudirin nasu baya wa Najeriya fatan alheri.

KU KARANTA: Matar aure ta yi wa diyar miji mugun duka, ta sheka lahira

2023: Ka taimakemu kada ka fito takara, za mu iya durkusawa gabanka - Fitaccen jigon Ibo ga Tinubu
2023: Ka taimakemu kada ka fito takara, za mu iya durkusawa gabanka - Fitaccen jigon Ibo ga Tinubu. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Bai dace da addini da dabi'a ba - Dr Hakeem ya caccaki shigar sirikar Atiku a ranar aurenta

A wani labari na daban, basarake a jihar Ogun, Joseph Ogunfuwa, ya nuna nadamarsa na yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen a 2015.

Ogunfuwa wanda ke da sarautar Babalaje na Remoland a jihar Ogun, ya ce Buhari ya bashi kunya tare da yawan 'yan Najeriya.

Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi ga jama'a a Sagamu domin bikin cikarsa shekaru 80 a duniya. Ogunfuwa ya ce Buhari da ya sani ba shi bane na yanzu da yake gani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel