Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga 4, sun ceto wasu wadanda aka yi garkuwa da su

Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga 4, sun ceto wasu wadanda aka yi garkuwa da su

- Rundunar sojojin OSS ta samu nasarar ceto mutane 4 daga hannun masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Dandume dake Katsina

- Rundunar ta kuma samu nasarar ragargazar 'yan ta'adda a maboyarsu dake Unguwan-Doka a karamar hukumar Faskari a jihar

- Shugaban rundunar, Birgediya janar Bernard Onyeuko ya roki jama'a mazauna yankin arewa maso yamma da su dinga ba wa jami'an tsaro hadin kai

Sojojin Najeriya sun tabbatar da rundunar OSS ta samu nasarar kashe 'yan bindiga 4 a Unguwar Doka dake karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina, duk a cikin shirin kawar da 'yan bindiga a arewa maso yamma.

Rundunar ta samu nasarar kubutar da mutane 4 da 'yan bindigan suka yi garkuwa da su 'yan kauyen Giruwa dake karamar hukumar Dandume a jihar.

Daraktan hukumar tsaro Birgediya janar Bernard Onyeuko, ya bayyanar da hakan a wata takarda da ya gabatar a Special Army Super Camp IV dake karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina.

Onyeuko ya tabbatar da cewa rundunar ta samu nasarar kashe wasu 'yan ta'addan a karamar hukumar Kurfi dake jihar, inda ta amso shanaye 43, awaki 6, tumaki 8 da bindigogin toka 2 a hannun 'yan ta'addan.

Ya ce: "A ranar 2 ga watan Oktoba 2020, rundunar OSS ta samu nasarar ceto mutane 4 'yan karamar hukumar Dandume daga hannun masu garkuwa da mutane a Sabon Layi, ta kuma samu nasarar yin kaca-kaca da wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne a Unguwan-Doka, inda aka cafke 4, sauran kuma suka tsere cikin daji."

Ya kara da bayyana yadda suka samu nasarar ceto mutane 4 da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su, wadanda suke tsare a hannun su na kwanaki 12 kuma sun sake su domin komawa ga iyalan su.

Ya tabbatar wa al'umma cewa sojoji za su cigaba da dagewa wurin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Ya kara da rokon jama'ar yankin arewa maso yamma da su dinga bada hadin kai ga jami'an tsaro don gano inda 'yan ta'adda suke.

KU KARANTA: Matar aure ta yi wa diyar miji mugun duka, ta sheka lahira

Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga 4, sun ceto wasu wadanda aka yi garkuwa da su
Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga 4, sun ceto wasu wadanda aka yi garkuwa da su. Hoto daga @Thisday
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta

A wani labari na daban, 'yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kai hari wasu yankuna biyu da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Kamar yadda Katsina Post ta wallafa, yankunan da aka kai harin sune Tsauwa da Gandu.

Jaridar ta wallafa cewa, a kalla rayuka tara suka salwanta yayin da wasu da yawa suka samu miyagun raunika kuma aka yi garkuwa da wasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel