Buhari ya yi alhinin rasuwar fitaccen dan wasan kwaikwayo Jimoh Aliu

Buhari ya yi alhinin rasuwar fitaccen dan wasan kwaikwayo Jimoh Aliu

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin fitaccen dan wasan kwaikwayo Jimoh Aliu

- Shugaban kasar ya yi waiwaye kan wasu muhimman gudunmuwa da Aliu ya bada a bangaren nishandantarwa na fiye da shekaru 50

- Buhari ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin ya kuma bawa iyalansa, masoyansa da sauran masu goyon bayansa hakurin rashi

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan Aliu, masana'antar masu nishadantarwa da gwamnatin jihar Ekiti bisa rashin fitaccen mai wasan drama, Jimoh Aliu.

Jimoh Aliu ya rasu yana da shekaru 80a duniya kamar yadda The Pulse ta ruwaito.

Buhari ya yi alhinin rasuwar fitaccen dan wasan kwaikwayo Jimoh Aliu
Buhari ya yi alhinin rasuwar fitaccen dan wasan kwaikwayo Jimoh Aliu. Hoto: @NigeriaGov
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kishi ya saka ango ya kashe amaryarsa da duka a wurin bikin aurensu a Rasha

Shugaban kasar cikin sanarwar da kakakinsa Femi Adesina ya fitar a ranar Talata a Abuja ya jinjinawa fasahar marigayin da ya kafa tawagarsa ta 'Jimoh Aliu Concert Party' a 1966.

Ya yabawa marigayin saboda irin gudunmawar da ya bayar a bangaren drama da nishadantarwa na fiye da shekaru 50.

A cewarsa, mutane da dama masoya drama da nishandantarwa za su yi kewan mutumin da aka fi sani da 'Aworo'.

KU KARANTA: Gowon ya bayyana halin da ya tsinci kansa lokacin da ya zama shugaban Najeriya yana dan shekara 31

Buhari ya jinjinawa marigayin da ya bayyana shi a matsayin mutum mai bawa masu yawa duba ya yi aiki a matsayin mai bada umurni, mai rubuta wasannin kwaikwayo, jarumi, da kuma mai sassaka gumaka.

Ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin yasa ya huta kuma Allah ya bawa wadanda ya bari a baya hakurin jure rashinsa.

Ya shirya fina-finai da dama ya kuma fito a matsayin jarumi, wasu daga cikinsu sun hada da Arelu, Yanpan, Yarin da Fopomoyo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel