Kamar Ganduje, Gwamna El-Rufai zai yi wa masarautar Zazzau garambawul

Kamar Ganduje, Gwamna El-Rufai zai yi wa masarautar Zazzau garambawul

- Akwai yiwuwar gwamnatin jihar Kaduna za ta rarraba masarautar Zazzau domin nada wasu sabbin sarakuna

- Hakan na zuwa ne bayan Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sanar da cewa gwamnatinsa na aiki kan wasu kudurori da za ta bawa majalisa don inganta mulki a jihar

- Wasu hasashe sun nuna cewa za a raba masarautar ta Zazzau ne zuwa gida uku - Masarautar Kaduna, Zazzau da Kudan kowanne da sarki

Gwamnatin Jihar Kaduna tana aiki kan wani kudirin doka da za ta yi garambawul ga yadda tsarin sarauta ya ke a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kudirin dokar na zuwa ne a lokacin da ake ganin akwai yiwuwar Gwamna Nasir El-Rufai yana kokarin rarraba masarautar Zazzau zuwa gida uku domin dukkan manyan masu neman zama sarki su samu sarauta.

Masarautar Zazzau ita ce mafi girma a jihar Kaduna, ta kunshi kananan hukumomi 11 da suka hada da Zaria, Sabon Gari, Giwa, Kudan, Makarfi, Ikara, Kubau, Soba, Igabi, Kaduna North da Kaduna South.

Kamar Ganduje, El-Rufai zai yi dokar rarraba masaruatr Zazzau
Kamar Ganduje, El-Rufai zai yi dokar rarraba masaruatr Zazzau. Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ka yi amfani da ICT don yakar 'yan ta'adda da 'yan bindiga - Tambuwal ga Buhari

A makon da ta gabata, Gwamna El-Rufai ya umurci masu zaben sarki na masarautar Zazzau su sake sabon zabe na wadanda ke neman zama sarki bayan rasuwar Alhaji Shehu Idris wadda ya rasu ranar 20 ga watan Satumba.

Ana rade-radin cewa gwamnatin jihar tana aiki kan wani kudiri na yi wa tsarin masarautar garambawul da za ta mika wa majalisar jihar don amincewa da shi a matsayin doka.

KU KARANTA: Kishi ya saka ango ya kashe amaryarsa da duka a wurin bikin aurensu a Rasha

Dokar inda ta samu amincewar majalisar za ta bada daman nada Magajin Gari, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Kaduna, Yariman Zazzau, Munnir Ja'afaru kuma a nada shi Sarkin Zazzau sai Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu a nada shi Sarkin Kudan a cewar rade-raden.

Yayin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2021, Gwamna Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na aiki kan kudirin yi wa masarautu garambawul da ake sa ran mika wa majalisar.

El-Rufai ya ce, "Za mu gabatar da wasu kudororin doka ga majalisar jihar da za su taimaka wurin inganta ayyukan gwamnati."

A wani rahoton daban, wata kotu da ke Malmo a kasar Sweden ta yanke hukuncin cewa musulmi suna da ikon su rika tafiya suyi salla a lokacin da suke wurin aiki.

Hukuncin ya ce dole masu kamfanoni su rika barin ma'aikatansu Musulmi su rika yin sallolinsu biyar a lokacin da suke wurin aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel