Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin mulkin Najeriya - Tanko Yakasai

Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin mulkin Najeriya - Tanko Yakasai

- Babban dan siyasa kuma daya daga cikin wadanda suka kafa Kungiyar Tuntuba ta Dattawan Arewa Tanko Yakasai ya yi martani ga masu matsa wa Buhari kan sauya fasalin tsarin mulki

- Yakasai ya ce shugaban kasa Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin mulkin kasar abinda zai iya kawai shine rubuta kudiri ya mika wa majalisa

- Yakasai ya ce kowanne dan Najeriya na iya rubuta kudirin ya bawa majalisar jiha ta na tarayya ta hakan ne za a iya samun sauyin

Alhaji Tanko Yakasai a ranar Litinin ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin mulkin Najeriya a karkashin kundin tsarin mulkin kasar.

Ya shawarci masu neman ganin an yi wa tsarin mulkin kasar garambawul su tabbatar wakilansu a majalisun jihohi da tarayya sun samar da dokokin da za su bada daman sauya mulkin kasar.

Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin Najeriya - Tanko Yakasai
Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin Najeriya - Tanko Yakasai. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kishi ya saka ango ya kashe amaryarsa da duka a wurin bikin aurensu a Rasha

A hirar da Yakasai ya yi da The Punch ta wayar tarho a Abuja ya ce, "Shugaban kasa ba shi da karfin ikon yi wa tsarin mulkin Najeriya garambawul.

"Abinda zai iya yi shine gabatar da kudirin neman yin hakan ga Majalisar Tarayya kamar yadda kowanne dan Najeriya ke da damar.

"Ina kira ga wadanda ke neman ganin an sauya fasalin tsarin mulkin kasar su matsa wa wakilansu na majalisun jihohi da tarayya lamba don ganin an yi hakan.

"Ya zama dole mu bi dokoki wurin ganin mun cimma abinda muke so. A halin yanzu mulkin demokradiyya muke yi da ke bukatar tattaunawa da tuntuba.

KARANTA NAN: Ka yi amfani da ICT don yakar 'yan ta'adda da 'yan bindiga - Tambuwal ga Buhari

"Ko wane matsala muke da shi, muna iya tunkarar 'yan majalisun mu domin tabbatar da cewa sun saurare mu."

Jami'in tuntubar na shugaban kasa a jamhuriya ta biyu ya ce za a fi samun cigaba a kasar idan ana tattaunawa a kan batutuwa domin cimma matsaya.

Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God Fasto Enoch Adeboye da wasu fitattun 'yan Najeriya a ranar Asabar sunyi kira ga shugaban kasar ya gaggauta yin garambawul ga tsarin mulkin kasar don kada ta tarwatse.

A wani rahoton, gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Alhamis ya sanar da sakin fursunoni 25, rage wa'adin wasu ciki har da waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa da aka sauya musu zuwa ɗaurin rai da rai.

Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin jawabinsa na bikin ranar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel