Shirin lamunin abincin duniya WFP ta fara raba kudi da abinci ga mutane 67,000 a Kano

Shirin lamunin abincin duniya WFP ta fara raba kudi da abinci ga mutane 67,000 a Kano

- Saboda irin bannar da annobar Korona ta yiwa rayukan mutane, majalisar dinkin duniya ta kawowa mutane Najeriya dauki

- Shirin lamunin abincin duniya zai taimakawa mutane 200,000 da kudi da abinci a jihohin Najeriya uku

- An zabi jihohin uku ne domin su suka fi girgiza a annobar cutar Korona

Shirin lamunin abincin duniya WFP ta kaddamar da raba kayayyakin tallafi ga mutane masu rauni da marasa karfi 67,000 da cutar COVID-19 ta shafa a jihar Kano.

A cewar wakilin WFP dake Najeriya, Paul Howe, ya ce asusun abincin zai isa ga jihohin da cutar Korona ta fi shafa ne irinsu Legas, birnin tarayya Abuja da jihar Kano, Humangle ta ruwaito.

Paul Howe, a taron kaddamar da rabon abincin a Kano ranar Litinin yace annobar COVID-19 ta haddasa matsaloli fiye da kiwon lafiya a fadin duniya.

Yace: "COVID-19 ta shafi bangaren noma, wannan shine karo na farko da WFP za ta bada tallafi ga birane."

"Amma, kimanin mutane 200,000 za'a taimakawa da kayan masarufi da kudi a Kano, Abuja da Legas.

"Tare da taimakon ton 2,000 na kayan hatsi da gwamnatin tarayya za tayi daga rumbun abincinta, za'a iya shawo kan matsalan noma a fadin kasar."

Paul ya ce za'a aiwatar da shirin domin yaye matsalolin da COVID-19 ta haifar.

DUBA NAN: Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2021 ranar Alhamis

Majalisar dinkin duniya ta kaddamar da taimakawa marasa karfi 67,000 a jihar Kano
Credit: @HumAngle
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ku maye gibin kujerun yan majalisar APC jihar Edo - PDP ga INEC

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya jinjinawa kungiyar bisa taimakonta ga marasa galihu.

Ya siffanta taimakon WFP a matsayin abin maraba da zai taimakawa mutane da dama wajen samun jarin farfado da kasuwancinsu.

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari yana neman izinin gabatar da kasafin kudin 2021 gaban majalisar dokokin tarayya ranar Alhamis, 8 ga Oktoba, 2020.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aikewa majalisar da safiyar Talata a zauren majalisa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel