Magidanci ya sanya wa jaririnsa suna Buhari saboda karrama shugaban kasa (Hotuna)

Magidanci ya sanya wa jaririnsa suna Buhari saboda karrama shugaban kasa (Hotuna)

- A ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoba wani magidanci Abdul dan jos ya rada wa dansa suna Buhari saboda kaunar da yake wa shugaba Buhari

- Dama ya rada wa dansa sunan ne bayan ya ji labarin yadda wani bakatsine ya sauya ra'ayinsa yasa wa dan sa Suleiman maimakon Buhari

- Kamar yadda Abdul yace, bayan jin wannan labarin ne ya lashi takobin sharewa Shugaba Buhari kukansa, yayi masa takwara

Wani Abdul dan Jos, jihar Plateau ya rada wa dan sa suna Buhari bayan yaji wani bakatsine ya sauya wa dansa suna daga Buhari.

A yadda bakatsinen yace, bai gamsu da yanayin mulkin shugaba Buhari bane shiyasa ya canja aniyar sa daga sawa dan sa Buhari ya maida shi Suleiman.

Abdul yace saboda tsananin son da yake wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rada wa jaririn da matarsa ta haifa masa sunan shugaban kasan.

Magidanci ya sanya wa jaririnsa suna Buhari saboda karrama shugaban kasa
Magidanci ya sanya wa jaririnsa suna Buhari saboda karrama shugaban kasa. Hoto daga Kabiru Sarkin Adoh
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sabon hari: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 9, sun raunata wasu tare da sace wasu a Katsina

Magidanci ya sanya wa jaririnsa suna Buhari saboda karrama shugaban kasa
Magidanci ya sanya wa jaririnsa suna Buhari saboda karrama shugaban kasa. Hoto daga Kabiru Sarkin Adoh
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rashawa: Sanatan APC zai mika bukatar yanke hannun masu satar kudin kasa

Magidanci ya sanya wa jaririnsa suna Buhari saboda karrama shugaban kasa
Magidanci ya sanya wa jaririnsa suna Buhari saboda karrama shugaban kasa. Hoto daga Kabiru Sarkin Adoh
Asali: Facebook

A wani labari na daban, John Oyegun, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya ce mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance mara sa'a tun farkon shi.

A yayin zantawa da manema labarai a gidansa da ke Benin a ranar Litinin, ya ce ba don salon mulkin ba, da Najeriya bata samu cigaban da ta samu a yanzu ba, The cable ta wallafa.

A yayin jajantawa a kan manyan kalubalen da suka addabi kasa, Oyegun ya ce wadanda ke mulki a yanzu ba su yin kokarin da ya dace kuma hakan ta sa 'yan Najeriya suka sare.

"Al'amura sun yi tsauri. Abinda zan iya cewa shine an gina ginshikin cigabanmu amma kuma mulkin nan babu sa'a," yace.

"Mun samu jarabawoyi masu tarin yawa tun daga farkon mulkin nan kuma duk da haka muna fuskantar cigaba. Babu shakka.

"Akwai yunwa, tattalin arziki baya habaka, rashin aikin yi, ta'addanci da sauransu. Dole ne in bayyana cewa, ina matukar damuwa da yadda komai ke tafiya," yace

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel