Matar aure ta yi wa diyar miji mugun duka, ta sheka lahira

Matar aure ta yi wa diyar miji mugun duka, ta sheka lahira

- Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa sun damke wata matar aure mai suna Aishatu Umaru

- Ana zargin matar da laifin kashe diyar mijinta wacce take riko a hannuta da mugun duka

- Matar ta musanta laifinta, inda tace mijinta baya basu abinci kuma hakan yasa yarinyar ke fama da ciwo

'Yan sandan jihar Adamawa sun damke wata matar aure da ake zargi da yi wa diyar mijinta dukan da yayi ajalinta.

Aishatu Umaru ta shiga hannun hukuma a ranar Alhamis bayan makwabta sun kai wa 'yan sanda koken zarginta da suke da kashe diyar mijinta mai suna Walida wacce take rikewa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje wanda ya zanta da manema labarai a Yola, ya tabbatar da kamen Aisha Umaru daga kauyen Kugama da ke karamar hukumar Mayobelwa ta jihar a kan laifin horo da yunwa da kuma kashe yarinyar.

Ya ce wacce ake zargin a halin yanzu ana tuhumarta a sashin laifuka na musamman kuma za a mika ta gaban kotu.

Matar aure ta yi wa diyar miji mugun duka, ta sheka lahira
Matar aure ta yi wa diyar miji mugun duka, ta sheka lahira. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon hari: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 9, sun raunata wasu tare da sace wasu a Katsina

Amma kuma ko da aka zanta da Aisha, ta musanta kashe Walida inda tace yarinyar tuntuni bata da lafiya amma mijinta ya hana kudin kai ta asibiti.

"Ban kasheta ba. Abinda ya faru shine, Walida ta saba zuwa makwabta. Sai na tura daya daga cikin yarana domin kiranta. Tana shigowa na dungure mata kai a matsayin fada, a take kuwa ta fadi.

"Sanin cewa bata da lafiya, sai na gaggauta zuwa gidan dan uwana amma sai na tarar baya nan.

"A lokacin da na dawo gida, na samu daya daga cikin makwabtana wacce tace min yarinyar ta rasu. Mijina ne ya janyo haka kuma bayan kama shi da aka yi an sakesa," ta bayyana.

KU KARANTA: Osinbajo ya magantu a kan yadda jami'an SARS ke azabtarwa da kashe 'yan Najeriya

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani- Kayode, yayi magana akan bidiyon da ya bayyana yana dukan matarsa, Precious Chikwendu.

Tsohon ministan yayi magana ranar Asabar akan bidiyon da yayi ta yawo a duniya wanda aka ganshi yana dukan matarsa, inda yace ya kama ta da namiji a gadonsu na sunna ne.

Fani-Kayode yayi maganar ranar Lahadi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Facebook akan al'amarin. Ya ce ya boye haukar matarsa na tsawon shekaru 7 ba tare da ya bayyanawa duniya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel