Kishi ya saka ango ya kashe amaryarsa da duka a wurin bikin aurensu a Rasha

Kishi ya saka ango ya kashe amaryarsa da duka a wurin bikin aurensu a Rasha

- Ango ya halaka amaryarsa a wurin bikin aurensu a kasar Rasha saboda tsabar kishi

- Ango ya rufe amaryarsa da duka ne saboda kishin wani mutum da ya hallarci daurin auren

- Amaryar ta hadu da angon ne a lokacin yana gidan yari amma ta yi imanin za ta iya taimaka masa ya canja halinsa

An kama wani mutum mai shekaru 33, Stepan Dolgikh saboda kashe matarsa mai shekaru 36 da duka a ranar aurensu a kauyen da ke Prokudskoye a kasar Rasha

Wasu da abin ya faru a idonsu sun ce mijin ya fara dukan matar ne saboda kishin daya daga cikin bakin da suka hallarci bikin daurin auren da aka yi a wani gida kamar yadda Dailymail.co.uk ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Matsalolin Najeriya: Rashin tunani zai sa a dora wa mulkin soja laifi - Babangida

Kishi ya saka ango ya kashe amarya da duka a ranar aurensu a Rasha
Kishi ya saka ango ya kashe amarya da duka a ranar aurensu a Rasha. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Ya zargi sabuwar matarsan da nuna halin 'rashin tarbiyya'.

Shugaban masu bincike Kirill Petrushin ya ce, "Ya fara naushinta da haurinta a wajen gidan.

"Ya dade yana dukan ta, a gaban shaidu, yana dukan ta gabanta da suka hada da kai da ciki.

"Ya amsa laifinsa a lokacin da ya ke amsa tambaya.

"Maganar tuba ... ba zan iya tsokaci a kai ba. Ni dai ban yarda ya tuba ba."

KARANTA NAN: Ka yi amfani da ICT don yakar 'yan ta'adda da 'yan bindiga - Tambuwal ga Buhari

Ya kara da cewa, "Yana cikin maye, saboda kishi, ya fusata ya fara cin zarafin matarsa.

"Yana kishi ne saboda daya daga cikin bakin da suka hallarci bikin auren. A tunanin mijinta bai gamsu da abinda tayi ba hakan ya janyo fitina."

Tunda farko, kotu ta taba samun mutumin da laifin kisa da fashi amma matar ta yi imanin za ta iya taimaka masa ya canja halayensa.

"Ta san cewa ya taba zuwa gidan yari.

"Sun hadu a lokacin yana gidan yari saboda laifin da ya aikata a baya," inji Petrushin.

A wani rahoton daban, wata kotu da ke Malmo a kasar Sweden ta yanke hukuncin cewa musulmi suna da ikon su rika tafiya suyi salla a lokacin da suke wurin aiki.

Hukuncin ya ce dole masu kamfanoni su rika barin ma'aikatansu Musulmi su rika yin sallolinsu biyar a lokacin da suke wurin aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel