2023: Atiku ya magantu a kan fastocin yakin neman zabensa

2023: Atiku ya magantu a kan fastocin yakin neman zabensa

- 'Yan Najeriya sun dade da fara mahawara da cacar baki a kan batun takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023

- Jama'a da dama na ganin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai sake neman takara a karkashin inuwar jam'iyyar PDP

- Sau biyu Atiku ya na shan kaye a takarar shugaban kasa da ya yi a baya a karkashin inuwar jam'iyyar ACN da PDP

Tsohon mataimakin Shugaban-ƙasa, Atiku Abukar, ya magantu a kan bayyanar wasu fastocin yaƙin neman zaɓensa da suka mamaye yanar-gizo tun satin da ya gabata.

A cikin wani jawabi da ya fito ranar Litinin, Atiku, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2019, ya nesanta kansa daga bullar fastocin.

A jikin fastocin, an gabatar da Atiku a matsayin mutum na kwarai da zai iya ceton Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, a yayin da yake maida martani a kan batun, ya ce hankalinsa yafi karkata wajen ganin jam'iyyarsa ta PDP ta samu nasarar lashe zaɓen jihar Ondo.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta samar da lambobin kira idan jami'anta sun ci zarafin mutum

Martanin ya fito ne ta hannun mai yaɗa labaran Atiku, Paul Ibe.

2023: Atiku ya magantu a kan fastocin yakin neman zabensa
Atiku da manyan APC a wurin auren dansa, Aliyu, da amaryarsa; Fatima Nuhu Ribadu
Asali: UGC

Acewar Ibe:"lokaci na ƙarshe da nayi magana, na ce Atiku a halin-yanzu yafi karkarta ga zaɓen Edo.

''Kuma mun gode Allah mun gama da Edo, PDP ta yi nasara.

"Yanzu, Atiku da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP, sun duƙufa a kan zaɓen jihar ondo.

DUBA WANNAN: Sabon shirin gwamnatin Buhari na samawa matasa 1,000,000 aiki a Nigeria

''Dukkanin waɗannan zaɓuka suna da muhimmanci saboda suna ƙarawa jam'iyyarmu ƙarfi a zaɓe mai ƙaratowa a shekarar 2023.

"Wannan ba shine lokacin tsayawar Atiku ba, ba batun zaben shekarar 2023 ake yi a halin yanzu ba"

"Kodayake, ko dama Atiku zai ƙara tsayawa neman takarar shugabancin ƙasa, ba zai fitar da fastoci ba tun yanzu"

''Kada mu yi riga malam masallaci da azarɓaɓi, mu fara gamawa da batun zaɓen jihar Ondo da ke gab da ƙaratowa"A cewar Ibe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel