Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta

Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta

- Bidiyon Amaryar da ta tsere a ranar aurenta, ya karade kafafen sada zumuntar zamani

- Amaryar ta tsere ne bayan ansa wayar da tayi lokacin da take hanyar zuwa daurin auren nata

- Kwatsam sai aka sanar da ita cewa saurayin da zata aura yana lalata da kawar ta

Wani bidiyon amaryar da ta tsere ranar aurenta bayan ta gano saurayin da zata aura yana tarayya da kawarta ya karade kafafen sada zumunta. Al'amarin ya faru ne a Area 2, a Garki jihar Abuja.

Kamar yadda aka wallafa a shafin sada zumunta, wata mata na cikin mota zata nufi wurin daurin aurenta, kwatsam sai aka kirata a waya.

Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta
Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

Inda aka sanar da ita cewa saurayin da zata aura yana lalata da kawarta ana saura kwanaki kadan a daura aurensu. Take anan amaryar ta dakatar da motar, ta tsere.

Bidiyon ya bayyana yadda kawayenta suka biyo bayanta don gudun kada taje ta salwantar da rayuwar ta.

Amaryar tayi ta kuka tamkar zata kashe kanta, inda kawayenta keta kokarin rarrashin ta.

KU KARANTA: Osinbajo ya magantu a kan yadda jami'an SARS ke azabtarwa da kashe 'yan Najeriya

KU KARANTA: Hotunan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani- Kayode, yayi magana akan bidiyon da ya bayyana yana dukan matarsa, Precious Chikwendu.

Tsohon ministan yayi magana ranar Asabar akan bidiyon da yayi ta yawo a duniya wanda aka ganshi yana dukan matarsa, inda yace ya kama ta da namiji a gadonsu na sunna ne.

Fani-Kayode yayi maganar ranar Lahadi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Facebook akan al'amarin. Ya ce ya boye haukar matarsa na tsawon shekaru 7 ba tare da ya bayyanawa duniya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel