Yanzu-yanzu: An sallami Donald Trump daga asibiti inda yake jinyar cutar Korona

Yanzu-yanzu: An sallami Donald Trump daga asibiti inda yake jinyar cutar Korona

- Shugaban kasan Amurka ya fara samun sauki da cutar Korona

- Likitansa ya bayyana cewa zai iya komawa gida amma zai cigaba da shan magani

An sallami shugaban kasar Amurka, Donald J Trump daga asibitin Sojojin Walter Reed dake Bethesda inda yake jinya bayan kasuwa da cutar Coronavirus.

Shugaban kasan da kansa ya bayyana hakan da yammacin Litinin a shafinsa na Tuwita.

Trump ya jaddada cewa ko kadan bai tsoron cutar Korona kuma ya yi kira ga mutane su daina tsoron cutar saboda ba komai bace.

"Zan bar asibitin Walter Reed yau daidai karfe 6:30 na yamma. Ina samun sauki. Ku daina tsoron COVID. Kada ku bari tayi tasiri a rayuwanki. Na fi jin dadi yanzu fiye da shekaru 20 baya." Yace

Likitan Donald Trump, Dr Sean Conley, ya ce shugaban kasan zai koma fadar White House duk da cewa "ba wai ya gama samun lafiya ba" kuma zai cigaba da shan manyan magunguna.

KU KARANTA: Sama da shekaru 7 nake rufa wa matata asiri saboda darajar 'ya'ya - Fani Kayode

Yanzu-yanzu: An sallami Donald Trump daga asibiti inda yake jinyar cutar Korona
Credit
Asali: UGC

A ranar Asabar, An tafi da Shugaba Donald Trump asibitin sojoji na Walter Reed. Hakan na zuwa ne bayan gwajin da aka yi wa shugaban na Amurka ya nuna ya kamu da cutar Covid 19 wato Coronavirus.

Asibitin sojojin yana wajen birnin Washington ne kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

DUBA NAN: Bai dace da addini da dabi'a ba - Dr Hakeem ya caccaki shigar sirikar Atiku a ranar aurenta

Idan za a iya tunawa Trump da mai dakinsa Melania sun kamu da korona a ranar Alhamis 2 ga watan Oktoba bayan wata hadimar shugaban, Hope Wicks ta kamu da cutar.

Kafin garzayawa da shi asibitin sojojin, an bawa shugaban na Amurka wasu magunguna.

Wannan bayanin na kunshe ne cikin wani sanarwa da likitan shugaban kasar ya fitar kamar yadda CNN ta ruwaito.

"A halin yanzu Shugaban kasa yana cikin yanayi mai kyau amma akwai gajiya tattare da shi. Wata tawagar kwararru na duba shi kuma tare da su zamu bada shawarar abinda ya dace a masa shi da mai dakinsa," a cewar likitan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel