Bai dace da addini da dabi'a ba - Dr Hakeem ya caccaki shigar sirikar Atiku a ranar aurenta

Bai dace da addini da dabi'a ba - Dr Hakeem ya caccaki shigar sirikar Atiku a ranar aurenta

- Dr Hakeem Baba-Ahmed, jigon APC a jihar Kaduna, yayi magana akan shigar diyar Ribadu ranar aurenta

- Ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda yace shigarta ta sha banban da koyarwar addininta da kuma al'adarta

- Ya kuma roki iyaye da kuma matasa da su daina kwaikwayon shigar yahudawa, wadda tayi karo da koyarwar Musulunci

Dr Hakeem Baba-Ahmed, jigon APC a jihar Kaduna, yace shigar auren Fatima Ribadu tayi hannun riga da koyarwar addini da kuma al'adarta.

Idan baku manta ba, shagalin bikin Aliyu Abubakar dan mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da diyar tsohon shugaban EFCC da akayi a Asokoro, Abuja ranar Asabar. ya samu halartar manyan baki.

Kyakyawar amaryar da ta gama Nigerian Turkish International College, dake Abuja a 2015, ta saka wata rigar amare wadda yanayin adonta na Dubai ne.

Hotunanta sun yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, inda musulmai suka yi ta sukar rigar, ana cewa bata dace da Musulinci ba.

KU KARANTA: Hotunan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga

Bai dace da addini da dabi'a ba - Dr Hakeem ya caccaki shigar sirikar Atiku a ranar aurenta
Bai dace da addini da dabi'a ba - Dr Hakeem ya caccaki shigar sirikar Atiku a ranar aurenta. Hoto daga arewafamilyweddings
Asali: Instagram

KU KARANTA: Osinbajo ya magantu a kan yadda jami'an SARS ke azabtarwa da kashe 'yan Najeriya

"Gabadaya bai dace da addini da kuma al'adarta ba," cewar Dr Hakeem Baba-Ahmed.

Dr Hakeem ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Lahadi, inda yake rokon iyaye da kuma matasa musulmai akan daina kwaikwayon al'adun yahudawa.

Kamar yadda ya wallafa, "A yau ne naga hotunan bikin wata yarinya musulma, tayi shiga wadda ta saba da addini da kuma al'adar ta."

Ya kara da cewa, "Irin haka yana tada min da hankali. Ina rokon iyaye da kuma matasa da su dena kwaikwayon al'adun da suka saba wa tamu."

Ya kuma roki masu bin shafinsa da kada suyi wani tsokaci na batanci a wallafar nan tasa ko kuma zagi.

Wani Harun Elbinawi yayi nasa tsokacin, inda yace, "A arewacin Najeriya, ana amfani da dokar shari'a ne akan talakawa.

"Suna zartar da dokar shari'ar musulinci ne akan talakawan arewacin Najeriya amma babu mai sabawa dokoki da tsarin addini kamar su.

"Sannan suna amfani da kalaman musulinci idan suna so su yaudari talakawa."

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani- Kayode, yayi magana akan bidiyon da ya bayyana yana dukan matarsa, Precious Chikwendu.

Tsohon ministan yayi magana ranar Asabar akan bidiyon da yayi ta yawo a duniya wanda aka ganshi yana dukan matarsa, inda yace ya kama ta da namiji a gadonsu na sunna ne.

Fani-Kayode yayi maganar ranar Lahadi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Facebook akan al'amarin. Ya ce ya boye haukar matarsa na tsawon shekaru 7 ba tare da ya bayyanawa duniya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel