Osinbajo ya kalubalanci tsarin da FG take bi wurin nade-nade

Osinbajo ya kalubalanci tsarin da FG take bi wurin nade-nade

- Yemi Osinbajo yace babban abinda ya kamata a kalla kafin a dora mutum a wani matsayi shine kwazonsa

- Mataimakin shugaban kasan ya fadi hakanne a wani muhimmin jawabi daya gabatar a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoba

- Osinbaji ya jaddada hakan saboda a cewarsa shugaba nagari na taimako wurin bunkasa tattalin arzikin kasa

Farfesa Yemi Osinbajo ya gabatar da wani jawabi a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoba, inda yace babban abinda ya dace a kalla idan za'a dora mutum a mukamin gwamnati shine kwazonsa, ba wani matsayin da ya taba rikewa ba a gwamnati.

Osinbajo ya fadi hakane a wani taro da NLI suka shirya, inda yace hakan zai taimaka wurin bunkasa tattalin arzikin kasa kamar yadda jaridar The Cable suka ruwaito.

Ya ce duk da taba rike mukamin mutum a kasa yana taimako wurin bashi ikon yin ayyuka yadda ya dace, amma idan aka nemi wakilci a wani wuri, su tabbatar sun zabi wanda yafi kowa nagarta.

Mataimakin shugaban kasa yace hakan ne zai taimaka wurin ciyar da kasa gaba.

A cewarsa: "Inaso in sassaita tunaninku akan abinda yafi dacewa a duba wurin zabar mutum a wani matsayi na gwamnati, ba makamin da ya taba rikewa kadai ya kamata a kalla ba,harda nagartarsa.

"Hakika nagarta tana da matukar muhimmanci, duk da sabawa da rike mukamai yana da amfani, amma halayya tafi komai.

"Misali, idan ana bukatar wata gunduma ta gabatar da wanda zai wakilceta, to wajibi ne su gabatar da wanda yafi kowa nagarta."

KU KARANTA: Budurwar da ke yi wa saurayinta girki ta kai masa ta gano cewa tare da wata yake ci

Osinbajo ya kalubalanci tsarin da FG take bi wurin nade-nade
Osinbajo ya kalubalanci tsarin da FG take bi wurin nade-nade. Hoto daga Vanguard
Asali: UGC

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya yi muhimmin kira ga shugabanni

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya tayi ala-wadai akan 'yan Najeriyan dake cewa Najeriya na gab da tarwatsewa.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya fadi hakanne a wata takarda ta ranar Lahadi, 14 ga watan Oktoba wanda yake cewa rashin kishin kasa ne furta wadannan kalamai.

Gwamnatin tarayya ta zargi wasu 'yan Najeriya akan maganganun nuna rashin kishin kasa. Garba Shehu ya ce gwamnatin Buhari ba za ta lamunci irin wadannan kalubalan ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel