Sama da shekaru 7 nake rufa wa matata asiri saboda darajar 'ya'ya - Fani Kayode

Sama da shekaru 7 nake rufa wa matata asiri saboda darajar 'ya'ya - Fani Kayode

- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya mayar da martani akan bidiyon da ya bayyana yana dukan matarsa

- Yace ya kama matarsa dare-dare akan gadon sunnarsu da wani kwarto suna cin amanarsa, amma duk da haka yayi shiru

- Yace masu yada wannan bidiyon don su zubar wa yaransa mutunci suke yi, shi kuma ba zai bayyana wani abu ba sai a gaban kotu

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani- Kayode, yayi magana akan bidiyon da ya bayyana yana dukan matarsa, Precious Chikwendu.

Tsohon ministan yayi magana ranar Asabar akan bidiyon da yayi ta yawo a duniya wanda aka ganshi yana dukan matarsa, inda yace ya kama ta da namiji a gadonsu na sunna ne.

Fani-Kayode yayi maganar ranar Lahadi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Facebook akan al'amarin. Ya ce ya boye haukar matarsa na tsawon shekaru 7 ba tare da ya bayyanawa duniya ba.

Ya ce wannan al'amarin ya bayyana ne don a bata min da kuma yarana suna a idon duniya.

Sama da shekaru 7 nake rufawa matata asiri saboda darajar 'ya'ya - Fani Kayode
Sama da shekaru 7 nake rufawa matata asiri saboda darajar 'ya'ya - Fani Kayode. Hoto daga @DailyNigerian
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hotunan mutum 11 da Matawalle ya ceto daga hannun 'yan bindiga

Kamar yadda Fani-Kayode ya bayyana, "Na zabi yin shiru akan rayuwata da ta iyali na, saboda kada mutuncinmu ya zube a idon duniya."

"Idan tana da wata damuwa, yakamata ta gabatar da ita a inda ya dace, a matsayinta na babba kuma uwa, ba wai ta dinga nuna wa duniya abinda zai bata wa yaranta suna ba.

"Nayi shiru don in rufawa yarana asiri, na rufe haukar da tayi ta nuna min na tsawon shekaru 7, ko sau daya ban taba bayyana wa ba. Amma inada shaidu da zan iya bayyana wa a kotu.

"Na yi magana ne don an matsamin inyi. Maimakon mu mayar da hankali akan damuwa da matsalolin kasar mu, mutanen Najeriya sunfi son yada wani al'amari mara dadi da ya faru da wani sanannen mutum," ya kara da cewa.

KU KARANTA: Bakar ranar ga Boko Haram: Dakarun soji sun ragargaza maboya da wasu 'yan ta'adda a Borno

A wani labari na daban, A cikin kwanakin nan ne aka dinga rade-radin rabuwar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da matarsa mai suna Precious Chikwendu.

Wannan lamarin ya janyo matukar cece-kuce daga jama'a da dama. Bayan fitowar rade-radin, tsohon ministan ya fito ya musanta rabuwarsu inda yace har yanzu suna tare.

A ranar Asabar da ta gabata kwatsam sai ga bidiyonsa yana dukanta inda take nadar bidiyon da kanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng