Rashawa: Sanatan APC zai mika bukatar yanke hannun masu satar kudin kasa

Rashawa: Sanatan APC zai mika bukatar yanke hannun masu satar kudin kasa

- Sanata Smart Adeyemi ya ce yana so a dawo da dokar yankewa barawo hannu a Najeriya

- Ya ce da zarar an yankewa ma'aikatan gwamnati 2 zuwa 3 hannaye, kowa zai shiga taitayin sa

- Sanatan ya kara da cewa, yana so yaransa su ji dadin Najeriya idan sun girma fiye da shi

Sanata Smart Adeyemi, sanatan dake wakiltar Kogi ta yamma, ya sanar da niyyarsa ta amince da mika dokar yankewa barawo hannu don kawar da rashawa a Najeriya.

Sanatan ya ce dokar zata sa barayi, musamman ma'aikatan gwamnati su daina sata.

A yadda ya ce, idan har aka yankewa wani ma'aikacin gwamnati a kasar nan hannu, dole kowa ya kiyaye.

Adeyemi ya sanar da niyyar nan tashi a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoba, a yayin tattaunawa da manema labarai a Lokoja, jihar Kogi, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Dan majalisar yace, da zarar an yankewa mutane 2 zuwa 3 hannu, dole sauran su shiga taitayinsu.

Ya ce, "Me nake magana akai? Mu mayar da hankulanmu akan yakar rashawa. Kwanan nan zan kawo bukatu na ga ICPC da EFCC zuwa majalisa.

"Inaso a kawo dokar yankewa barawo hannu, wato shari'ar Musulinci. A lokacin da aka yankewa mutane 10 zuwa 20 hannaye a kasar nan, babu wanda zai sake sata."

"A lokacin da aka ce mutane 2 zuwa 3 sun fuskanci hukuncin nan mai tsanani, ko a yankewa mutum hukuncin noma Acre 200 zuwa 250 na gona, yadda barawon zai kare rayuwarsa yana mana noma." Inji Adeyemi.

Ya kara da cewa yana so Najeriya ta bunkasa, saboda idan yaranshi suka girma suji dadi fiye da shi.

KU KARANTA: Bakar ranar ga Boko Haram: Dakarun soji sun ragargaza maboya da wasu 'yan ta'adda a Borno

Rashawa: Sanatan APC zai mika bukatar yanke hannun masu satar kudin kasa
Rashawa: Sanatan APC zai mika bukatar yanke hannun masu satar kudin kasa. Hoto daga @SenSmartAdeyemi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kano: Hotunan jami'an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sanda, M.A Adamu ya dakatar da ma'aikatan FSARS daga cigaba da ayyukansu, sakamakon korafin da 'yan Najeriya suke yi akan 'yan sanda na ta'addanci.

Ba su kadai wannan umarnin ya shafa ba, har da ma'aikatan STS, IRT da kuma ACS. An dakatar da ma'aikatan daga yin ayyuka kamar sintiri, tsayawa bincike, ba da hannu da sauran ayyukan da suke yi a kan tituna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng