Da duminsa: IGP Adamu ya haramta wa jami'an SARS wasu jerin ayyuka

Da duminsa: IGP Adamu ya haramta wa jami'an SARS wasu jerin ayyuka

- Shugaban 'yan sanda, IGP Muhammed Adamu ya dakatar da ma'aikatan FSARS akan cigaba da ayyukansu

- Ya kuma dakatar da su akan saka kayan gida yayin da suke sintiri da kuma ayyukan kan titi

- An bada wannan umarnin ne bayan 'yan Najeriya sun yi ta korafi akan 'yan sandan na ta'addanci

Sifeta janar na 'yan sanda, M.A Adamu ya dakatar da ma'aikatan FSARS daga cigaba da ayyukansu, sakamakon korafin da 'yan Najeriya suke yi akan 'yan sanda na ta'addanci.

Ba su kadai wannan umarnin ya shafa ba, har da ma'aikatan STS, IRT da kuma ACS.

An dakatar da ma'aikatan daga yin ayyuka kamar sintiri, tsayawa bincike, ba da hannu da sauran ayyukan da suke yi a kan tituna.

Sakamakon rashin sanin makaman aiki irin na su kamar yadda a kan samu lauyoyi, 'yan kasuwa, fastoci da sauran su suke yi.

Sannan shugaban 'yan sandan ya dakatar da duk wani dan sanda da yin sintiri ko kuma wasu ayyukan 'yan sanda da kayan gida. Dole ne su dinga saka kayan aiki.

KU KARANTA: Da asusun bankunan fastoci muke amfani don guje wa jami'an tsaro - Dan damfarar yanar gizo

Da duminsa: IGP Adamu ya haramta wa jami'an SARS wasu jerin ayyuka
Da duminsa: IGP Adamu ya haramta wa jami'an SARS wasu jerin ayyuka. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Nigeria @ 60: Muhimman abubuwa 7 a jawabin Buhari

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki.

Ya ce hakan kuwa daidai yake da kowacce kasa domin kuwa dukkan duniya ne ake cikin wannan halin.

Buhari ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga 'yan Najeriya a ranar da kasar ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai. Shugaban kasar ya kara da amincewa da cewa, kasar na fuskantar matsalolin tsaro daban-daban a sassan kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel