Bidiyo: Abubuwan al'ajabi da baku sani ba game da Shugaba Buhari
- Ko a cikin sa'oinsa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi zarra kuma ya tsaya ba kamar sauran ba
- Ya yi shugaban kasa a zamanin mulkin sojoji, shugaban PTF da kuma shugaban kasa na farar hula
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da abubuwa masu tarin al'ajibi a tattare da shi
A duk lokacin da aka fara magana a kan tarihin Najeriya, dole ne a kira sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Hakan ta kasance ne sakamakon rawar da ya taka a wasu muhimman abubuwan da suka faru kuma suka sauya akalar kasar nan baki daya.
Daga zamansa shugaban kasa a yayin mulkin soja har zuwa rike shugabancin PTF da yayi, da kuma zamansa shugaban kasa a karkashin mulkin fara hula.
Dole a ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi zarra cikin sa'o'insa da kuma sauran takwarorinsa a duniya.
Ga bidiyon wasu abubuwan al'ajabi da baku sani ba game da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
KU KARANTA: Fyade: Kotu ta kori soja daga aiki, ta yanke masa hukuncin shekaru 5 a gidan yari

Asali: UGC
KU KARANTA: Da asusun bankunan fastoci muke amfani don guje wa jami'an tsaro - Dan damfarar yanar gizo
A wani labari na daban, a ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki.
Ya ce hakan kuwa daidai yake da kowacce kasa domin kuwa dukkan duniya ne ake cikin wannan halin.
Buhari ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga 'yan Najeriya a ranar da kasar ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai. Shugaban kasar ya kara da amincewa da cewa, kasar na fuskantar matsalolin tsaro daban-daban a sassan kasar.
Ya ce, "A yau na tabbatar da cewa Najeriya tana cikin mawuyacin hali na tattalin azriki kuma hakan ce ta kasance ga kowacce kasa a fadin duniya. Muna fuskantar kalubalen tsaro a sassa daban-daban na kasar nan."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng