Bidiyon tsohon ministan Najeriya yana dukan matarsa ya janyo cece-kuce
- Rade-radin rabuwar auren tsohon ministan sufurin jiragen sama da matarsa na cigaba da yaduwa
- Duk da ministan ya fito ya musanta hakan, a ranar Asabar wani bidiyo ya fito wanda ya karade kafafen sada zumuntar zamani
- A bidiyon, an ga tsohon ministan Femi Fani-Kayode yana dukan matarsa yayin da yake mata magana a fusace
A cikin kwanakin nan ne aka dinga rade-radin rabuwar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da matarsa mai suna Precious Chikwendu.
Wannan lamarin ya janyo matukar cece-kuce daga jama'a da dama.
Bayan fitowar rade-radin, tsohon ministan ya fito ya musanta rabuwarsu inda yace har yanzu suna tare.
A ranar Asabar da ta gabata kwatsam sai ga bidiyonsa yana dukanta inda take nadar bidiyon da kanta.
Hakan ya sa jama'a sun yi caa a kansa inda suke kallonsa da wani ido na daban, duk kuwa da darajarsa da kuma babban mukamin da ya rike a kasar nan.
KU KARANTA: Fyade: Kotu ta kori soja daga aiki, ta yanke masa hukuncin shekaru 5 a gidan yari
KU KARANTA: Da asusun bankunan fastoci muke amfani don guje wa jami'an tsaro - Dan damfarar yanar gizo
A wani labari na daban, tsohon ministan harkokin sufurin sama, Femi Fani Kayode (FFK), ya musanta jita-jitar da ake yadawa a kan cewa yana shirin sake aure duk da har yanzu da sauran rigima tsakaninsa da tsohuwar matarsa da yanzu basa zaune tare.
A ranar Litinin ne tgsohon ministan ya yada wani hotonsa tare da wata kyakyawar budurwa da aka gano cewa sunanta Halima Yusuf.
Ganin hotunan tare da zukekiyar budurwar sun haddasa cece-kuce da yada gulmar cewa FFK na shirin sake yin aure a karo na biyar.
FFK ya yada hotunan ne daidai lokacin da rikicinsa da matarsa ta hudu, Precious Chikwendu, suke kara zafi, wata alama da ke nuna cewa aurensu ya lalace.
Sai dai, da ya ke mayar da martani a kan cecekucen da jama'a ke yi, FFK ya karyata jita-jitar cewa aure zai kara tare da bayyana cewa Halima ''kawatace da ke da kusanci da ni, na yarda da ita.''
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng