Boko Haram: MNJTF ta nemi taimakon sojojin kasar Kamaru

Boko Haram: MNJTF ta nemi taimakon sojojin kasar Kamaru

- Dakarun sojojin hadin gwiwa na kasa da kasa, MNJTF, ta nemi taimakon rundunar sojojin Kamaru don yaki da Boko Haram

- Kwamandan MNJTF, Ibrahim Yusuf ne ya yi wannan rokon yayin da ya ziyarci Gwamna Midjiyawa Bakari a Maroua ranar Asabar

- Yusuf ya ce taimakon da sojojin Kamaru na Sector 1 na MNJTF suka bada ne ya taimaka 'yan ta'adda da yawa suka mika wuya

Dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa da ke yaki da Boko Haram (MNJTF) ta tuntubi rundunar sojojin kasar Kamaru ta taimaka mata a yakin da ta ke yi da 'yan ta'addan Boko Haram a Najeriya.

Wannan na cikin wata sanarwar ce da kakakin MNJTF Kwanel Muhammad Dole ya fitar a ranar Asabar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Boko Haram: MNJTF ta nemi taimakon sojojin kasar Kamaru
Boko Haram: MNJTF ta nemi taimakon sojojin kasar Kamaru. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ka yi amfani da ICT don yakar 'yan ta'adda da 'yan bindiga - Tambuwal ga Buhari

Sanarwar ta ce kwamandan rundunar, Manjo Janar Ibrahim Yusuf ya yi wannan rokon ga Gwamna Midjiyawa Bakari yayin da ya tafi ziyarar aiki na kwana uku a Maroua a ranar Asabar.

Yusuf ya mika godiyarsa bisa taimakon da sojojin sector 1 na MNJTF suka yi wadda hakan ya taimaka wurin ayyukan sojojin har ta kai ga wasu yan taaddan sun mika wuya.

Ya ce samun goyon bayan mutanen yankin yana da muhimmanci wurin nasarar kawar da 'yan ta'addan.

Kwamandan ya bukaci kwamandojin sojojin Najeriya da na MNJTF su rika ziyartar juna daga lokaci zuwa lokaci domin kara fahimtar juna da amfana da juna.

KU KARANTA: Gowon ya bayyana halin da ya tsinci kansa lokacin da ya zama shugaban Najeriya yana dan shekara 31

Wani sashi na sanarwar ya ce, "Yana da muhimmanci a gane cewa ayyukan sector 1 MNJTF (Kamaru na da ka alaka da sauran dakarun sojoji a Kamaru. Wannan sun hada da Operation Emergence da Operation Alpha da sojojin ke yi a Maroua."

Tunda farko, Bakari ya yabawa MNJTF saboda samar da tsaro da tsaro a yankin Tafkin Chadi.

Bakari ya mika godiyarsa bisa dukkan sadaukarwar da sojojin MNJTF ke yi sannan ya basu tabbacin ayyukan da suke yi zai kawo zaman lafiya da cigaba a yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel