Yayinda ake shirin bude makarantu, kungiyar SSANU da NASU zasu tafi yajin aiki gobe

Yayinda ake shirin bude makarantu, kungiyar SSANU da NASU zasu tafi yajin aiki gobe

- Da alamun daliban jami'a zasu koma makaranta babu dukkan ma'aikata

- Yayinda ASUU ta jaddada cigaba da kasancewarta a yaji, SSANU da NASU zasu shiga

- Dukkansu sun mika bukatunsu ga gwamnatin tarayya

Kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya SSANU da kungiyar ma'aikata maras karantarwa NASU zasu shiga yajin aikin makonni biyu daga 5 ga Oktoba zuwa 19 ga Oktoba.

A jawabin da shugaban SSANU, Samson Ugwoke, da sakatare janar na NASU, Peter Adeyemi, suka rattafa hannu, sun ce zasu tafi yajin aiki ne saboda matsalolin da ake fuskanta da manhajar biyan albashi na IPPIS.

Sun ce manhajar ta haifar da matsaloli daban-daban wajen biyan albashi da alawus na mambobinsu.

Daga cikin matsalolin da aka ambata cikin jawabin sune, "rashin biyan mafi karancin albashi da kuma fansho da gratutin mambobinmu."

"Ku sani cewa zamu yi yajin aikin gargadi kafin mu tafi yajin aikin din-din-din idan ba'a magance matsalolin da muka ambata ba," jawabin yace

KU DUBA: Talaka ya kada ya damu da karin farashin man fetur saboda ba mota ko Janareto gareshi ba - Garba Shehu

Yayinda ake shirin bude makarantu, kungiyar SSANU da NASU zasu tafi yajin aiki gobe
Yayinda ake shirin bude makarantu, kungiyar SSANU da NASU zasu tafi yajin aiki gobe
Asali: UGC

KU KARANTA: Aliyu da Fatima: Hotuna daga auren Turakin Adamawa da diyar Nuhu Ribadu

Yayin hira da manema labarai bayan ganawar a jami'ar Legas ranar Juma'a, shugabannnin SSANU da NASU shiyyar Legas, Olusola Sowunmi da Kehinde Ajibade, sun ce yanzu ba zasu amince da IPPIS ba saboda gwamnati ta karya alkawarinta na magance matsalolin da ta haifar.

Sowunmi yace, "Bamu ji dadin yadda abubuwa ke gudana ba. IPPIS ta bamu kunya saboda mambobinmu da sukayi ritaya basu samun fanshonsu lokacin da ya kamata. Hakazalika ba'a biyanmu mafi karancin albashin da sauran ma'aikatun gwamnati ke samu."

Ajibade ya ce idan gwamnati ta iya nemo hanyar biyan sauran ma'aikata mafi karancin albashi, toh su ma a biyasu.

A bangare guda, kasa da sa'o'i 24 bayan gwamnatin tarayya ta sanar da bude dukkan makarantu, kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta ce malamanta ba zasu koma makaranta ba sai an biya bukatunsu.

Shugaban ASUU na kasa, Farfesa biodun Ogunyemi, ya tunatar da gwamnatin tarayya da iyayen yara cewa lakcarorin sun shiga yajin aiki ne saboda an ki amsa bukatunsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel