Talaka kada ya damu da karin farashin man fetur saboda ba mota ko Janareto gareshi ba - Garba Shehu

Talaka kada ya damu da karin farashin man fetur saboda ba mota ko Janareto gareshi ba - Garba Shehu

- Garba Shehu ya bayyana cewa mazauna birane ke amfana da man fetur ba na karkara ba

- A cewarsa, karin farashin ba zai shafi talakawa ba saboda basu da kayan alatun dake bukatar mai

Fadar shugaban kasa bata gushe ba tana kare karin farashin man fetur, yayinda mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya kara jaddada muhimmancin hauhawar.

Garba Shehu ya ce yawancin yan Najeriya basu amfani da man fetur saboda haka ba zasu amfana da rashin tsadarta ba, hakazalika tashin farashin ba zai shafesu ba.

Gwamnatin Buhari a farkon shekarar nan ta bayyana shirinta na cire tallafin mai tare da sauye-sauye a bangaren mai.

Tun daga lokacin farashin ya dan sauka bisa ga saukar farashin danyar mai a kasuwan duniya sakamakon bullar cutar Korona.

Amma a watan Satumba, farashin ya fara hauhawa kuma hakan ya tayarwa yan Najeriya hankali.

Wasu sun daurawa gwamnatin laifin bari farashin ya tashi duk da cewa yan Najeriya na fama da tasirin annobar Korona a rayuwarsu.

KU KARANTA: Takarar Atiku a 2023: Uwar jam'iyyar PDP ta yi fashin baki

Talaka ya daina kuka kan karin farashin man fetur saboda ba mota ko Janareto gareshi ba - Garba Shehu
Credit: @channelstv
Asali: Facebook

KU DUBA: Aliyu da Fatima: Hotuna daga auren Turakin Adamawa da diyar Nuhu Ribadu

A ranar Juma'a. yayin hira a shirin Politics Today a tashar ChannelsTV, mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu, ya ce babu adalci ace talakawa su cigaba da baiwa mazauna birni tallafi.

"Shin yan Najeriya nawa suka mallaki mota? Yan Najeriya nawa ke amfani da Janareto a gidajensu da suke bukatar mai? Shin akwai adalci manomi da makiyayi da talakawa, a rika daukan kudinsu ana biyan tallafin mai ga mazauna birni?" Shehu ya ce

"Saboda haka shugaban kasa na kokarin fito da komai fili ne kan lamarin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel