Aliyu da Fatima: Hotuna daga auren Turakin Adamawa da diyar Nuhu Ribadu

Aliyu da Fatima: Hotuna daga auren Turakin Adamawa da diyar Nuhu Ribadu

- 'Yayan manyan yan siyasa a jihar Adamawa Atiku Abubakar da Nuhu Ribadu sun yi daurin aure

- Hotunan auren Fatima da Aliyu sun jawo cece kuce a kafofin sada zumuntta

- Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu kan daurin auren tsakanin 'yayan yan jam'iyyun hamayya

An yi daurin aure tsakanin Turakin Adamawa, 'dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Fatima, diyar tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa EFCC, Nuhu Ribadu.

Hotunan daurin auren da ke gudana yau Asabar a birnin tarayya sun bayyana a shafukan ra'ayi da sada zumunta.

Yayinda angon ya sanya shadda har da rawani, amaryar ta sanya kayan turawa irin wanda amare ke sanyawa a coci.

KARANTA: Ba zamu koma aji ba sai an biya mana bukatunmu - Kungiyar ASUU ta yi tsokaci kan bude makarantu

KU DUBA: Takarar Atiku a 2023: Uwar jam'iyyar PDP ta yi fashin baki

Aliyu da Fatima: Hotuna daga auren Turakin Adamawa da diyar Nuhu Ribadu
Credit: Aliyu ahmad
Asali: Facebook

Aliyu da Fatima: Hotuna daga auren Turakin Adamawa da diyar Nuhu Ribadu
Photo: Instagram/@ijeomadaisy
Asali: Instagram

Kamar yadda aka saba, yan Najeriya dake sassa daban-daban sun tofa albarkacin bakinsu kan kayan da amaryar tasa

Yayinda wasu ke fadin cewa sun mata kyau, wasu sun ce wannan ba al'adar Fulani bace kuma ba'a kyauta ba.

Karanta abinda wasu suka fadi:

baeli.cious tace: "Ahap, Ribadu mai rajin tabbatar da Shari'ar Musulunci kuma kalli yadda diyarsa tayi wanka kamar wata 'Kim' ranar aurenta. Akwai munafurci a kasar nan."

ogooezeani yace: "Tayi matukar kyau... kamar fa zan mayar da hankali Arewa yanzu."

glorycofficial tace: "Tufafinta yayi matukar kyan gaske."

Mun kawo muku cewa Jiga-jigan Jam'iyyun APC Da PDP sun ajiye siyarsu gefe guda yayinda suka halarci daurin auren 'dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar Da 'Yar tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa, Nuhu Ribadu.

An daura auren Aliyu Atiku Abubakar ne da Fatima Nuhu Ribadu a yau Asabar a Aso Drive dake Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel