Zaben Ondo: Mataimakin Akeredolu, Ajayi ya zargi gwamnan da bannatar da N900m duk wata

Zaben Ondo: Mataimakin Akeredolu, Ajayi ya zargi gwamnan da bannatar da N900m duk wata

- Ana zargin Gwamna Akeredolu na bannatar da kudin kimanin Naira miliyan 900 da ya ke samu kowane wata

- Zargin ta fito ne daga bakin mataimakin gwamna, Ajayi, cikin wata sanarwar da ya yi game da kudaden jihar Ondo

- Ajayi ya yi wannan zargin ne bayan Gwamna Akeredolu ya bayyana cewa mataimakinsa na samun Naira miliyan 13 duk wata

Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi, ya zargi gwamna Rotimi Akeredolu da bannatar da kudaden da ya ke samu a jihar kowanne wata.

A cewar Ajayi, Akeredolu yana samun zunzurutun kudi Naira miliyan 900 duk wata kuma bannatar da kudin ya ke yi.

Zaben Ondo: Mataimakin Akeredolu, Ajayi ya zargi gwamnan da bannatar da N900m duk wata
Zaben Ondo: Mataimakin Akeredolu, Ajayi ya zargi gwamnan da bannatar da N900m duk wata. Hoto: @RotimiAkeredolu/@AAjayiAgboola
Asali: Twitter

The Nation ta ruwaito cewa bayyanan da Ajayi ya gabatar cikin sanarwar da kakakinsa Allen Sowore ya fitar ya yi ikirarin Akeredolu na samun N750m a matsayin kudin tsaro sai N150m a matsayin kudin gudanar da harkokinsa.

DUBA WANNAN: Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya

Ya ce, "Gwamnan yana samun N750m a matsayin kudin tsaro duk wata. Shi, Akeredolu kuma ana samun kudin gudanar da harkokinsa kimanin N150m."

Har ila yau, mataimakin gwamnan ya yi zargin cewa iyalan gwamnan suna karbar wasu kudade da suke juya wa da kansu.

Ajayi ya kara da cewa gwamnan yana bannatar da kudaden habaka garuruwan da ke kusa da rafi a jihar inda ya ke bannatar da kasonsu na 13%.

KU KARANTA: Kotu ta bawa musulmi damar zuwa Sallah a lokutan aiki a Sweden

Ya kuma gargadi gwamnan ya dena cacakarsa a kafar watsa labarai idan kuma bai bari ba zai cigaba da tona asirin gwamnatin.

A martaninsa, Gwamna Akeredolu ya musanta dukkan zargin na Ajayi. Da ya ke magana ta bakin Kakakinsa, Segun Ajiboye, gwamnan ya ce kowa yana iya duba bayanan da kansa ya tabbatar da gaskiya.

A wani labarin, Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Munnir Dan'iya ya kare kansa game da aikin ginin titi mai tsawon kilomita 1.530 da ake gina wa zuwa fadar sarkin Yamman Kware, Alhaji Muhammad Dan'iya.

Alhaji Muhammadu Dan'iya, wanda shine mahaifin mataimakin gwamnan yana daya daga cikin sabbin hakiman da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya nada kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel