Jiga-jigan APC da PDP sun ajiye siyasa gefe, sun halarci auren 'dan Atiku da diyar Nuhu Ribadu

Jiga-jigan APC da PDP sun ajiye siyasa gefe, sun halarci auren 'dan Atiku da diyar Nuhu Ribadu

- An yi daurin auren diyar Alhaji Nuhu Ribadu da Alhaji Atiku Abubakar

- Akalla manyan yan siyasa 10 ne suka halarci daurin auren da aka yi a Abuja

- Ba bu alaman bada tazara a taron amma an sanya takunkumin rufe baki

Jiga-jigan Jam'iyyun APC Da PDP sun ajiye siyarsu gefe guda yayinda suka halarci daurin auren 'dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar Da 'Yar tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa, Nuhu Ribadu.

An daura auren Aliyu Atiku Abubakar ne da Fatima Nuhu Ribadu a yau Asabar a Aso Drive dake Abuja.

Daga cikin manyan yan siyasan da suka halarci bikin sun hada da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso; tsohon shugaban jam'iyyar APC, Bisi Akande; gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i.

Sauran sune jigon jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu; gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; Sanata Uba Sani da gwamnan jihar Adamawa, Ahmed Fintiri.

Hakazalika akwai gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal; tsohon gwamnan Neja, Talban Minna; tsohon dan takaran gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

KU KARANTA: Ba zamu koma aji ba sai an biya mana bukatunmu - Kungiyar ASUU ta yi tsokaci kan bude makarantu

Jiga-jigan APC da PDP sun ajiye siyasa gefe, sun halarci auren 'dan Atiku da diyar Nuhu Ribadu
Credit: Aliyu ahmad
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sabbin mutane 126 sun kamu da Korona, yayinda ake gab da isa 60,000

Jiga-jigan APC da PDP sun ajiye siyasa gefe, sun halarci auren 'dan Atiku da diyar Nuhu Ribadu
Credit: Aliyu Ahmad
Asali: Facebook

Jiga-jigan APC da PDP sun ajiye siyasa gefe, sun halarci auren 'dan Atiku da diyar Nuhu Ribadu
Credit: Aliyu Ahmad
Asali: Facebook

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel