Kotu ta umurci a ajiye mata basarake mai shekaru 69 a gidan yari a Kogi

Kotu ta umurci a ajiye mata basarake mai shekaru 69 a gidan yari a Kogi

- Kotun majistare da ke Lokoja a jihar Kogi ya bada umurnin a bawa wani basarake da wasu mutum 10 masauki a gidan gyaran hali na sati biyu

- Hakan na zuwa ne bayan an shigar da karar tuhumar basaraken Momoh Nasir da laifin taimakawa wasu mutane wurin kai wa wasu da ke ibada hari haka sidan

- Ana tuhumar basaraken da sauran mutane 10 da yunkurin aikata kisa, hadin baki wurin aikata laifi, taimakawa wurin laifi da sauransu

Wata kotu da ke Lokoja a ranar Juma'a 2 ga watan Oktoba ta bada umurnin ajiye wani mai rike da saurautar gargajiya mai shekaru 69 a karamar hukumar Adavi, Asema Uka (Otumi-Ajoko) Momoh Nasir da wasu mutum 10 a gidan yari kan zargin kisa.

'Yan sanda suna tuhumar basaraken da wadanda ya hada baki da su da laifin yunkurin kisar kai, hadin baki don aikata laifi, bada taimako wurin aikata laifi wadda ya saba wa wasu sassa na Penal Code a jihar Kogi.

DUBA WANNAN: Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya

Kotu ta tura basarake mai shekaru 69 da wasu mutum 10 zaman wucin gadi a gidan yari
Kotu ta tura basarake mai shekaru 69 da wasu mutum 10 zaman wucin gadi a gidan yari. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Alkaliyar kotu, Agatha Shankyula ta bada umurnin a basu masauki a gidan yarin gwamnatin tarayya da ke Koton-Karfe a jihar Kogi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA: Kotu ta yi watsi da bukatar neman rusa wani masallaci mai dimbin tarihi a India

A yayin da ke bada umurnin, Ms Shankyula ta ce abinda ake zarginsu da aikatawa babban laiffi ne kamar yadda aka bayyana a takardar karar saboda haka akwai bukatar a zurfafa bincike.

Tunda farko, dan sanda mai shigar da kara Tuesday Ganagana shaidawa kotun cewa wanda ake zargin a ranar 28 ga watan Satumba sun kai wasu mutane hari yayin da suke ibadah a Kabba Junction don zaben kananan hukumomi da za ayi a watan Disamba a jihar.

Mai shigar da karar ya yi ikirarin cewa wani Momoh Nasiri ya taimaka wa wadanda ake zargin da ke dauke da bindiga, sanda, wuka, duwatsu da adda sun afka wurin da ake ibadan sun raunata mutum takwas.

Lauyan wadanda ake tuhumar, Mu'azu Abbas ya roki kotun ta bada belin wadanda ya ke karewa.

A wani rahoton daban, Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Alhamis ya sanar da sakin fursunoni 25, rage wa'adin wasu ciki har da waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa da aka sauya musu zuwa ɗaurin rai da rai.

Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin jawabinsa na bikin ranar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴanci. Read more:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel