Sarkin Musulmi ya yi muhimmin kira ga shugabanni

Sarkin Musulmi ya yi muhimmin kira ga shugabanni

- Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na III ya yi muhimmin kira ga shugabanni

- Ya yi kira garesu da su kwatanta adalci da daidaito a tsakanin mabiyansu

- Ya yi wannan kiran ne yayin bikin bude Masallacin Juma'a na fadar masarautar Kaena a jihar Nasarawa

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar II, ya yi kira ga shugabanni na kananan hukumomi, jihohi da tarayya da su tabbatar da wanzuwar adalci da daidaito domin tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.

Ya yi wannan kiran ne yayin bikin bude masallacin Jeans da ke fadar Osana na Keana da ke karamar hukumar Kena ta jihar Nasarawa a ranar Juma'a

Basaraken, wanda shin shugaban majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci, ya ce, "Ina kira ga 'yan Najerta da su guji hada al'amuran siyasa da addini kuma su cigaba da yi wa shugabanninsu addu'a.

"Ina jinjinawa jama'a karamar hukumar Kaena a kan zaman lafiyar da suka runguma duk da banvancinsu a addini.

"Ina kara kira da a saka darussan tarihi a makarantu domin a samu abin sanar da nna baya a kan zaman lafiyar da magabatnasu suka yi," yace.

A jawabinsa, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya jinjinawa Sarkin musulmin a kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya.

KU KARANTA: Kano: Gagarumin dan fashi da makami, Maikudi, ya sanar da sirrin aika-aikarsa

Sarkin Musulmi ya yi muhimmin kira ga shugabanni
Sarkin Musulmi ya yi muhimmin kira ga shugabanni. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Budurwar da ke yi wa saurayinta girki ta kai masa ta gano cewa tare da wata yake ci

A wani labari na daban, kungiyar matasan arewacin Najeriya (CNNY), ta bukaci tsohon gwamnan jihar Abia, gwamna Orji Uzor Kalu ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2023.

Batun Wanda zai maye gurbin shugaban kasa Muhammad Buhari yana ta matsowa saboda saura shekaru 3 wa'adin mulkinsa ya cika.

Hakan zai bai wa 'yan kudancin Najeriya damar fitar da gwaninsu. Jiga-jigan jam'iyyar APC irin su Asiwaju Bola Tinubu ne ake sa ran zasu amshi kujerar mulki da zarar wa'adin shugaba Buhari ya kare a 2023.

CNNY ta ce zasu rike wuta yadda Kalu, wanda yanzu haka sanata ne daga jihar Abia zai maye gurbin shugaban kasa a 2023.

CNNY sun sanar da hakan a wata takardarsu ta ranar 1 ga watan Oktoba, wadda shugaban su Zarewa Salisu Sageer da sakataren su na kasa, Abu Bature Dandume suka sa hannu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel