Ina alfahari da ayyukan cigaban da muka yi wa Najeriya tare da Obasanjo - Atiku

Ina alfahari da ayyukan cigaban da muka yi wa Najeriya tare da Obasanjo - Atiku

- Atiku Abubakar ya ce yana matukar alfahari da ayyukan da suka yi da tsohon shugaban kasa Obasanjo daga 1999 zuwa 2007

- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce sun biya dukkan basussukan da ake bin Najeriya a zamaninsu

- Kalaman Atiku sun zama tamkar martani ga kalaman Buhari inda ya dora laifin nakasar da kasar ke ciki a kan shuwagannin da suka gabata

Atiku Abubakar, ya yi alfahari da nasarorin da suka samu a karkashin mulkin Olusegun Obasanjo.

Obasanjo da Atiku Abubakar sun mulki kasar nan a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa daga shekarar 1999 zuwa 2007.

A wata wallafar da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 2 ga watan Oktoba, Atiku ya ce mulkinsu ya biya dukkan bashin da ake bin kasar nan sannan ana samun cigaba a fannin tattalin arziki da kashi 6 a kowacce shekara.

Kamar yadda wallafar ta bayyana: "Tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, Najeriya ta biya dukkan bashin da ake bin ta kuma ta cigaba da samun cigaban tattalin arziki da kashi 6.

"Wadannan ne lokutan gyara kuma ina matukar alfahari da aiki tare da shugaban kasa Obasanjo da kuma irin ayyukan da muka yi wa kasar nan."

KU KARANTA: Kano: Gagarumin dan fashi da makami, Maikudi, ya sanar da sirrin aika-aikarsa

Ina alfahari da ayyukan cigaban da muka yi wa Najeriya tare da Obasanjo - Atiku
Ina alfahari da ayyukan cigaban da muka yi wa Najeriya tare da Obasanjo - Atiku. Hoto daga @AtikuAbubakar
Asali: Twitter

KU KARANTA: An kama dan sandan da je rubuta wa wani jarababawar UTME ta 2020

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a, 25 ga watan Satumba, ya ce ya dauka alhakin lallasa APC da aka yi a zaben ranar Asabar da ta gabata na gwamnoni.

Shugaban kasar ya sanar da hakan a gidan gwamnati bayan karbar sabon gwamna jihar Edo, Godwin Obaseki, tare da mataimakinsa Philip Shaibu da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP.

Buhari ya ce a matsayinsa na babban jiigo a jam'iyyarsa, shine yakamata a dora wa laifin komai ballantan a lokacin da aka lallasa su a zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel