An kama dan sandan da je rubuta wa wani jarababawar UTME ta 2020

An kama dan sandan da je rubuta wa wani jarababawar UTME ta 2020

- Hukumar JAMB ta tabbatar da cafke wani dan sanda da take zargi da basaja yayin jarabawar 2020

- Ta zargi dan sandan mai suna Etim Israel da yin sojan gona wurin rubuta wa wani jarabawa kuma har ya samu 240

- Rikicin ya fara ne yayin da yaje neman gurbin karatu a jami'a amma aka tabbatar masa da cewa ba hotonsa bane

Hukumar jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB), ta damke wani jami'in dan sanda mai suna Etim Israel, a kan zarginsa da ake da shiga rubutawa wa wani jarabawar 2020.

A yayin jawabi ga manema labarai a Abuja, shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce dan sandan na daya daga cikin masu rubuta jarabawar 657 da suka bukaci sauya hoto bayan kammala rijista ba tare da wani dalili ba.

Israel dan sanda ne mai mukamin Constable kuma yana aiki a ofishin hukumar ne da ke Akwa Ibom, ya yi rijistar da sunan wanda zai rubuta wa tare da hotonsa da sauran abubuwan bukata.

Ya samu maki 240 kuma ya yanke hukuncin fara neman gurbin karatu a makarantar daga da sakandaren, Channels TV ta wallafa.

Amma kuma, rikicin ya fara ne lokacin da aka sanar da shi cewa ba zai iya cigaba ba saboda banbancin hotonsa da na mai neman gurbin karatun.

Babu kakkautawa ya kama hanyar zuwa ofishin JAMB don mika kokensa, lamarin da ya saka shi cikin wani hali har aka kama shi.

KU KARANTA: Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta

An kama dan sandan da je rubuta wa wani jarababawar UTME ta 2020
An kama dan sandan da je rubuta wa wani jarababawar UTME ta 2020. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rufe sashin tsokaci a Twitter: 'Yan Najeriya sun caccaki Shugaba Buhari

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnoni da gwamnoni 'yan uwansa sun jawa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum kunne akan ya dinga tsananta tsaro musamman idan zai je wurare masu hadarin gaske, amma sai yace "ya batun mutane na na jihar Borno? Me zai faru dasu?"

A wannan halin tashin hankalin dake Borno. Fayemi yayi wannan maganar ne ranar Laraba yayin da ya jagoranci tafiya tare da gwamnan Sokoto, wanda shine mataimakin shugaban NGF, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, wanda shine shugaban gwamnonin APC da kuma Simon Lalong na jihar Plateau, wanda yake shugabantar NGF, zuwa jihar Borno don jajantawa Zulum akan harin da 'yan ta'adda suka kai wa tawagarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel