Shugaba Buhari ya nada Yusuf Jibrin sabon shugaban asibitin koyarwa ta ATBU

Shugaba Buhari ya nada Yusuf Jibrin sabon shugaban asibitin koyarwa ta ATBU

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dakta Yusuf Jibrin a matsayin sabon shugaban asibitin koyarwa ta Jamiar Tafawa Balewa da ke Bauchi

- Ministan Lafiya, Dakta Osagie Ehanire ne ya sanar da nadin a ranar Jumaa 2 ga watan Oktoba a babban birnin tarayya Abuja

- Dakta Osagie ya shawarci sabon shugaban ya zama mai adalci da gaskiya ya kuma san cewa shugaban kasa ya ke wakilta don shi ya nada shi

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dakta Yusuf Jibrin a matsayin shugaban asibitin koyarwa na Jamiar Tafawa Balewa, ATBUTH da ke Jihar Bauchi.

Ministan Lafiya, Dakta Osagie Ehanire ne ya tabbatar da hakan a ranar Jumaa a Abuja inda ya ce nadin da aka masa na shekaru hudu ne kuma zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Satumban 2020.

DUBA WANNAN: Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya

Buhari ya nada Yusuf Jibrin sabon shugaban asibitin koyarwa ta ATBU
Buhari ya nada Yusuf Jibrin sabon shugaban asibitin koyarwa ta ATBU. Hoto @daily_nigerian
Source: Twitter

Da ya ke mika sakon shugaban kasar ga Jibrin, ministan ya ce ya sani cewa babban kalubalen da ke gabansa shine kulawa da wadanda ke karkashinsa.

"Za ka rika kula da kayayyaki, kudade, da kuma babban cikinsu mutane wanda shine mafi wahala."

Ya shawarci sabon shugaban asibitin ya sani da cewa ba an nada shi bane don kansa.

KU KARANTA: Mataimakin gwamnan Sokoto ya kare kansa game da fitar da N718m don ginin titi zuwa fadar mahaifinsa

"Kana jagoranci ne a madadin shugaban kasa. Ya kamata ka sani wani ne ya amince da nadin ka. Duk abinda kayi, nauyin na kan wuyan shugaban kasa," kamar yadda ya masa gargadi.

Mista Ehanire ya shawarci sabon shugaban ya rika bawa kowa girmansa ya kuma yi aiki lafiya da kowa har da kwararru da yan siyasa da sauran mutane.

A jawabinsa, Sanata Olorunnimbe Mamora, karamin Ministan Lafiya ya bukaci Jibrin ya sani cewa "mulki amana ce."

Mista Mamora ya kuma tunatar da sabon shugaban cewa ba shi kadai bane mutumin da ya cancanci nadin saboda haka dole ya yiwa kowa adalci.

A bangarensa, Mista Jibrin ya mika godiyarsa bisa shawarwarin da suka bashi ya kuma yi alkawarin zai yi iya kokarinsa don ganin ya sauke nauyin da aka daura masa.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji shugaban jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, na kasa Farfesa Tunde Adeniran a ranar Talata ya sanar da cewa ya yi murabus daga harkokin siyasa ta hammaya.

Adeniran ya sanar da hakan ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannunsa da kwanan watan 29 ga watan Satumban 2020 da ya aike wa hedkwatan jam'iyyar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel