Yanzu-yanzu: Yan fashi sun kai farmaki banki, sun yi awon gaba da makudan kudi

Yanzu-yanzu: Yan fashi sun kai farmaki banki, sun yi awon gaba da makudan kudi

- Kwana baya bayan sakon yan sanda, yan fashi sun dira wani banki a jihar Ekiti

- Sun yi harbe-harbe amma basu kashe kowa ba, kuma sun rarike makudan kudi

- Mazauna yankin sunce cikin mintuna 40 da sukayi suna fashin, babu dan sandan da ya leko

Yan fashi sun kai farmaki bankin WEMA dake Iyin-Ekiti, karamar hukumar Irepodun/Ifelodun na jihar Ekiti da yammacin Juma'a, 2 ga watan Oktoba, 2020.

Yan fashin guda shida sun dira wajen ne misalin karfe 3:30 na rana inda suka fasa kofofin bankin da nakiya.

Sun yi awon gaba da miliyoyi kuma sun kwashe mintuna 40 suna fashin, Jaridar The Nation ta ruwaito.

Wannan fashin ya faru kimanin awanni 24 bayan da yan sanda suka sanar da cewa da alamun yan bindiga na kokarin kai hari jihar.

Wani mai idon shaida ya bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan shun shiga suna harbin kan mai uwa da wabi domin fitittikar mazauna da yan kasuwan dake wajen.

Yanzu-yanzu: Yan fashi sun kai farmaki banki, sun yi awon gaba da makudan kudi
Yanzu-yanzu: Yan fashi sun kai farmaki banki, sun yi awon gaba da makudan kudi
Asali: Original

KU KARANTA:Kamuwa da Coronavirus: Buhari ya jajantawa Donald Trump kuma yayi masa addu'a

A cewar majiyar, "Gaskiya yan sanda sun bamu kunya. Yan fashin sun kwashe mintuna 40 suna cin karansu ba babbaka."

"Sun zo cikin motoci biyu, suna harbi sama suna tsorata mutane."

"Ofishin yan sandan ke Igede-Ekiti bai kai nisan mita 500 yayinda mazaunar yan sanda masu sintiri bata wuce nisan kilomita daya ba, amma babu wanda ya zo cikinsu na tsawon minti 40 da yan fashin ke fashi."

"Amma mun gode babu wanda aka kashe, amma harbe-harben ya razana mutane."

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar da labarin inda yace yan sanda sun isa wajen da wuri.

"Mun samu rahoto daga Iyin Ekiti kan fashin kuma da wuri muka tura jami'anmu dake wajen. Ina tabbatar muku cewa ana bibiyan yan fashin domin tabbatar da cewa an kamasu," Yace

A bangare guda, A cigaba da ƙoƙarin ta na dakile ta'addanci, Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe ƴan bindiga 312 ta kuma ceto mutum 91 da aka yi garkuwa da su a arewa maso gabashin kasar tsakanin watan Yuli zuwa Satumba.

Da ya ke yi wa ƴan jarida jawabi a Abuja, Kakakin Hedkwatar Tsaro, Manjo Janar John Enenche ya ce an kashe ƴan ta'adda da dama an kuma lalata maɓuyarsu ta harin sama, ƙasa da na ruwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel