Kano: Gagarumin dan fashi da makami, Maikudi, ya sanar da sirrin aika-aikarsa

Kano: Gagarumin dan fashi da makami, Maikudi, ya sanar da sirrin aika-aikarsa

- Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta damke gagarumin dan fashi da makami da ya addabi jihar Kano

- An gano cewa dan fashin da makami dan asalin jihar Katsina ne kuma yana da shekaru 27 da haihuwa

- Ya sanar da cewa, yana dirkawa jama'a miyagun kwayoyi ne da farko kafin ya kwashe kudadensu

Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta damke wani mutum da ake zargi da fashi da makami tare da kwarewa wurin bai wa wadanda ya kama miyagun kwayoyi.

Wanda ake zargin mai suna Abdullahi Maikudi mai shekaru 27 dan asalin jihar Katsina ne, kuma an kama shi tare da wani Rabiu Abdullahi mai shekaru 23 dan asalin jihar Kano.

An kama su da laifin satar kudi har naira miliyan shida daga wani dan kasuwa a garin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Kakakin rundunar 'yan sandan, ASP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, ya ce jami'an 'yan sanda ne suka damkesu.

Jami'an 'yan sanda na yankin Minna sun kai samame inda suka samu naira miliyan uku da dubu dari takwas da kuma Cefa 410 daga wurinsu.

Kamar yadda ASP Abiodun ya sanar, Maikudi ya sauka a wani otal a Tegina, inda ya hadu da dan kasuwar a ranar 25 ga watan Satumba.

An gano cewa ya bibiyi dan kasuwar har suka dasa abota inda yace masa daga jiha daya suke.

A yayin tattaunawar ne ya bai wa dan kasuwar shayi mai dauke da miyagun kwayoyi. Dan kasuwar ya kwanta bacci mai nauyi bayan shan shayin sannan ya kwashe masa kudi.

KU KARANTA: Rufe sashin tsokaci a Twitter: 'Yan Najeriya sun caccaki Shugaba Buhari

Kano: Gagarumin dan fashi da makami, Maikudi, ya sanar da sirrin aika-aikarsa
Kano: Gagarumin dan fashi da makami, Maikudi, ya sanar da sirrin aika-aikarsa. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna)

A wani labari na daban, wani bakaniken kan hanya dake unguwar Nkwola Eziama a jihar Imo ya gudu da motar wadanda suka bashi gyara.

Kamar yadda wani mawaki ya wallafa ranar Asabar, 26 ga watan Satumba, wata Chinyere Ezeji ta ce motarsu ta tsaya a wuraren layin Amala/Eziama ranar Juma'a.

Sai suka dakata wurin bakaniken kan hanyar Nkwola-Eziama, mai suna Chukwudi don ya gyara musu motar.

Bayan ya tattaba motar, sai yace bari ya zagaya da ita don ya tabbatar ko gyaran yayi, daga nan ba'a sake ganinshi ba.

"Muna hanyar zuwa kauyenmu ta'aziyya da motar Rev. Cyril Nwaelele, sai motar ta samu matsala a hanyar Amala/Eziama.

"Wasu mutanen kirki suka taimakemu wurin tura motar zuwa Nkwola-Eziama, inda muka samu bakanike wanda yayi kokarin gyara motar daga nan ya wuce da ita.

"Mun samu labarin sunan mutumin Chukwudi kuma dan Omoku ne. Don Allah, idan an samu wanda ya sanshi, ya taimakemu mu amso motar", yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel