Nigeria @60: Gwamnoni sun aike da muhimmin sako ga 'yan Nigeria

Nigeria @60: Gwamnoni sun aike da muhimmin sako ga 'yan Nigeria

A ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, Nigeria ta yi bukin cika shekaru 60 da samun 'yanci daga Turawan mulkin mallaka, bikin da 'yan Nigeria suka nuna murnarsu ta fuskoki da dama.

A bangarorin gwamnati kuwa, baya ga jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a Abuja, suma gwamnonin jihohin Nigeria, sun aike da sako ga al'umar kasar.

A yayin da wasu gwamnonin ke mika sakon gaishe gaishe da bayar da shawarwari ga, wasu kuma, suna mika kokon bara ne ga gwamnati na ayyukan da jihohin su ke bukata.

Shuwagabannin da suka shude suna da rauni wajen daukar tsauraran matakai, cewar Gwamna Abiodun

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ce shuwagabannin da suka shude suna da rauni wajen daukar tsauraran matakan da suka dace, kuma su ya kamata a kama da laifukan yanzu.

KARANTA WANNAN: Dalilin da ya sa gwamnatin Buhari ta cancanci yabo daga yan Nigeria - Malami

Gwamnan ya bayyana hakan a ranar Alhamis a lokacin da ya jagoranci majalisar zartaswar gwamnatinsa zuwa filin taron murnar cika Nigeria shekaru 60 da samun yanci a Abeokuta.

Gwamnan ya ce duk da cewa kasar tana fuskantar matsaloli daban daban, sai dai, an samu ci gaba mai yawa, da ya kamata yan Nigeria su yi farin ciki domin su.

Nigeria @60: Gwamnoni sun aike da muhimmin sako ga 'yan Nigeria
Nigeria @60: Gwamnoni sun aike da muhimmin sako ga 'yan Nigeria - @ekitistategov
Source: Twitter

Gwamna Wike ya kawo bukatar tabbatar da mulkin karba karba a kasar

A jihar Rivers, Gwamnan Nyesom Wike ya ce Nigeria ba za ta taba ci gaba ba har sai an tabbatar da tsarin mulkin karba karba a kasar.

Wike ya bayyana bukatar hakan a jawabinsa na murnar cikar Nigeria shekaru 60 da samun yanci, a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal, a ranar Alhamis.

KARANTA WANNAN: Buhari ya yi amai ya lashe ana gobe bikin Nigeria @60

Ya ce akwai kuma bukatar yan Nigeria su fuskanci matsalolin siyasa da tattalin arziki da suka yiwa kasar katutu, kuma aka kasa magance su.

Gwamna Diri ya roki zaman lafiya, soyayya a tsakanin yan Nigeria

A jihar Bayelsa, Gwamna Douye Diri ya bukaci yan Nigeria da su mayar da hankali wajen wanzar da zaman lafiya da kuma soyayya a tsakaninsu, domin samar da al'umma ta gari.

A sako ta kafofin rediyo da aka yada a ranar Alhamis, domin murnar shekaru 60 da samun yancin Nigeria, da kuma cikar Bayelsa shekaru 24 da samu, Diri ya ce, bai kamata wani ya kyamaci wani ba.

Ka da ku yake kanwa da samun kyakkyawar Nigeria, Gwamna Obaseki ya bukaci matasa

A jihar Edo kuwa, Gwamna Godwin Obaseki a ranar Alhamis, ya bukaci 'yan Nigeria musamman matasa da ka da su cire tsammani da samun kyakkyawar Nigeria da suke mafarkin samu.

Da ya ke jawabi a gidan gwamnatin jihar da ke Benin, a yayin da Nigeria ke murnar cika shekaru 60 da samun yanci, Obaseki, ya ce idan aka hada kai, to za'a kai tudun mun tsira a kasar.

Gwamna Zulum ya yi kira ga yan Nigeria da su sake damarar nuna kishi da hadin kai

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umar Zulum, a ranar Alhamis, ya yi kira ga yan Nigeria da su sake damarar nuna kishin kasa da hadin kai a tsakanin su.

Gwamnan a cikin sakon taya Nigeria murnar cika shekaru 60 da samun yanci, kuma ya yiwa shugaban kasa Buhari da yan Nigeria fatan alkairi na tsinkayar wannan rana.

Ku sake gina babbar hanyar Benin zuwa Warri, Okowa ya roki Gwamnatin tarayya

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake gina babban titin Benin zuwa Warri, yana mai cewa, titin ya lalace.

Ya kuma bukaci gwamnati da ta mayar da hankali kan titin Agbor zuwa Eku da ke a cikin jihar, yana mai nuni da cewa, shima titin ya lalace, yana bukatar gyara cikin gaggawa.

A wani labarin, Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na kasa, Abubakar Malami ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi aikin azo a gani, bai kamata a zage ta ba, in har ba za a yaba mata ba.

Ya ce ya kamata mambobin jam'iyya mai mulki a kasar, su yi tunkaho da alfahari da gwamnati mai ci, la'akari da ayyukan raya kasa da ta shimfida a cikin yan shekarun nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel