Dalilin da ya sa gwamnatin Buhari ta cancanci yabo daga yan Nigeria - Malami

Dalilin da ya sa gwamnatin Buhari ta cancanci yabo daga yan Nigeria - Malami

- Abubakar Malami (SAN) ya ce idan har yan Nigeria ba za su iya godewa gwamnatin shugaba Buhari ba, to bai kamata su zagi mulkin sa ba

- Malami ya yi nuni da cewa, gwamnatin APC ta kawo ci gaba maras misaltuwa a Nigeria, kama daga bunkasa rayuwa, gine gine, samar da ayyuka, da magance tsaro

- Haka zalika, Antoni Janar na kasar, ya bukaci 'yan Nigeria sun alkalanci kan halin da kasar take ciki kafin zuwan APC, da kuma halin da kasar ta ke ciki a yanzu

Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na kasa, Abubakar Malami ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi aikin azo a gani, bai kamata a zage ta ba, in har ba za a yaba mata ba.

Ya ce ya kamata mambobin jam'iyya mai mulki a kasar, su yi tunkaho da alfahari da gwamnati mai ci, la'akari da ayyukan raya kasa da ta shimfida a cikin yan shekarun nan.

Malami ya bayyana hakan ne a lokacin da ya marabci mambobin kungiyar kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC (Non-NWC NEC) a ofishinsa da ke Abuja.

KARANTA WANNAN: Buhari ya yi amai ya lashe ana gobe bikin Nigeria @60

Idan ba za ku yabawa gwamnatin APC ba, to bai kamata ku zage ta ba - Malami
Idan ba za ku yabawa gwamnatin APC ba, to bai kamata ku zage ta ba - Malami - @TheNationNews
Source: Twitter

A baya bayan nan gwamnatin ke shan suka sakamakon tabarbarewar tattalin arziki, rashin tsaro, talauci, cin hanci da rashawa da kuma rashin gine ginen ci gaban kasa.

Sai dai Malami ya ce: "Jam'iyyarmu ta yi kokari matukar gaske. Muna da labaruka masu dadi da zamu iya bayarwa, kuma muna da hujjoji da zamu iya nuna na ayyukan da muka yi.

KARANTA WANNAN: Ana shirin murnar Nigeria @60, gwamnatin Ogun ta sanya dokar ta baci

"A shekarar 2018 shugaban kasa Buhari ya kwato $322m daga Switzerland, inda ya kaddamar da shirye shiryen bunkasa jama'a da kudin, kamar shirin N-Power da sauransu.

"Haka zalika, shugaban kasar ya kaddamar da shirin ciyar da daliban makarantun Firamare da kuma na Sakandire.

"Sannan muna da shirin TraderMoni, wanda ya tallafawa kananu da matsakaitan 'yan kasuwa daga kananan hukumomi 774 na fadin kasar.

"Kuma idan za a tuna, gwamnati mai ci ta gaji rashin ayyukan yi, basussuka, da matsaloli masu yawa daga gwamnatin baya, amma duk da haka, ta cimma nasarori masu yawa."

A wani labarin, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ba da tabbacin cewa Boko Haram ta kusa zama tarihi a mulkin Buhari, kasancewar yan ta'adda ba za su iya fin karfin shugabanni da mabiyansu ba.

Buni ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Maiduguri yayin jajantawa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, kan harin da Boko Haram ta kai wa tawagarsa a hanyar zuwa Baga.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel