Kotu ta yi watsi da bukatar neman rusa wani masallaci mai dimbin tarihi a India

Kotu ta yi watsi da bukatar neman rusa wani masallaci mai dimbin tarihi a India

- Kotu a kasar Indiya ta yi watsi da karar da wasu masu addinin hindu suka shigar na neman a rushe wani masallaci mai dimbin tarihi

- Masu addinin hindun sun yi ikirarin cewa wani sashi na masallacin ya ratsa cikin wurin bautar su da ke dauke da kabarin abin bautarsu 'Lord Krishna'

- Mahukunta na wurin bautar ta Katra Keshav Dev sun ce za su daukaka kara zuwa kotu na gaba tunda ba su gamsu da hukuncin ba

Kotu ta yi watsi da bukatar neman rusa wani masallaci mai dimbin tarihi a India
Kotu ta yi watsi da bukatar neman rusa wani masallaci mai dimbin tarihi a India. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ashariyar da wasu aku 5 ke yi wa mutane a gidan zoo yasa dole an raba su (Hotuna)

Wata kotu a birnin Mathura da ke arewacin Indiya ta yi watsi da karar da aka shigar na rushe wani masallaci da ke kusa da mahaifar Lord Krishna da ke wurin bautar hindu na Katra Keshav Dev.

"Za mu daukaka kara zuwa kotu na gaba duba da cewa akwai wasu abubuwa masu muhimmanci da kotun ba ta yi la'akari da su ba," a cewar lauyan mai shigar da kara, Hari Shankar Jain.

A makon da ta gabata, wasu mutane sun tafi kotun kan wani masallaci da aka gina shi karni na 17 mai suna Shahi Idgah inda suka yi ikirarin an gina shi ne a mahaifar Lord Krishna, wani babban abin bauta na masu addinin Hindu da ke harabar wurin bauta na Katra Keshav Dev.

KU KARANTA: Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya

A cikin karar da suka shigar a kotun, masu karar sun nemi a soke yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Shri Krihna Janmasthan Seva Sansthan da Kwamitin masallacin Shahi Idgah na yin gini a wani fili kusa da wurin bautan.

Masu shigar da karar sun nemi kotun ta umurci kwamitin masallacin "su rushe duk wani gini da suka yi da ya shiga filin da ke harabar wurin bautan na Katra Ksehav Dev."

Har wa yau, masu karar sun nemi a hana wadanda aka yi karar da masu kare su da ma'aikatansu da masu goyon bayansu da duk wani mai wakiltansu daga kusantar harabar wurin bautar mai girman acre 13.37.

A wani rahoton,Yan sanda a Enugu sun kama wani mutum da ya shiga wani wurin bauta ya kama abin bautar da ya ce ya hana mutanen garin cigaba, ya yi sanadin tabarbarewar kasuwanci tare da hana 'yan mata samun mazan aure.

Mutumin mai matsakaicin shekaru, Nnajiofor Donatus ya ce wahayi aka masa ya tafi ya cire abin bautar daga inda ya ke.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel