Jamhuriyyar Oduduwa: Babu ruwanmu da shirin ballewa daga Najeriya - Gamayyar Musulman yankin Yarbawa

Jamhuriyyar Oduduwa: Babu ruwanmu da shirin ballewa daga Najeriya - Gamayyar Musulman yankin Yarbawa

- Kungiyoyi daban-daban na kira ga ballewar Yarbawa daga Najeriya kamar yadda Igbo ke yi

- Tuni har an samar da sunan sabuwar kasa, jamhurriyar Oduduwa

- Amma Yarbawa Musulmai sun yi watsi da lamarin inda suka ce basu son wani sabon yakin basasa

Gamayyar Musulman Kudu maso yammacin Najeriya wato yankin kabilar Yoruba da kungiyar dalibai Musulman na yankin kudu sun nesanta kansu daga kiraye-kirayen da ake yi na ballewa daga Najeriya.

Wasu kungiyoyi a kasar Yarbawa suna kira ga kafa sabuwar kasa mai zaman kanta da suna jamhurriyar Oduduwa.

Tsokaci kan hakan, gamayyar Musulman yankin MUSWEN ta ce babu ruwanta da wannan abu da ake kullawa kuma ba zata sa baki cikin wani abu ba illa abin ya tattari magance matsalolin da kowa ke fama da shi a kasar gaba daya.

A cewar MUSWEN, akwai abubuwan da suka fi ballewa daga Najeriya muhimmanci.

DUBA NAN: Sai da aka gargadi Zulum kada ya tafi Baga amma yayi kunnen jaki - Tsohon dirakta a DSS

Jamhuriyyar Oduduwa: Babu ruwanmu da shirin ballewa daga Najeriya - Gamayyar Musulman yankin Yarbawa
Credit: Eagle Online
Source: UGC

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bada umurnin bude dukkan makarantu a Najeriya

A jawabin da gamayyar ta saki, tace: "Ga dukkan alamu, akwai makarkashiya a salo da usulubin da ake bi na kokarin kafa jamhuriyyar Oduduwa, musamman ma dukkan masu yakin haka yan addini guda ne."

"Wannan yunkuri da suke yi na nuna cewa akwai wata manufa daban na kafa kasar Yarbawa da zai iya haddasa yaki musamman na addini."

A bangaren shugaban kungiyar dalibai Musulmai na jihar Legas, Miftahudeen Thanni, yace: "Bamu shirya rashin mambobinmu ba kuma babu wani abin alfahari wajen yaki. Masu rajin sabuwar kasa su daina kuma su nema wani hanya daban na neman kudinsu."

"Bamu shiryawa wani sabon yakin basasa ba ko kashe-kashe a kudu maso yamma ba. Dukkanmu shaidu ne kan abinda ke faruwa a kudu maso gabas. Kawai mu mayar da hankali wajen hadin kai da fahimtar juna"

A wani labarin daban, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya sanar da umurnin bude dukkan makarantun Firamare, Sakandare, da jami'o'i a Najeriya.

Adamu ya sanar da hakan ranar Juma'a a hira da manema labarai a birnin tarayya Abuja, Premium Times ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel