Kotu ta bawa musulmi damar zuwa Sallah a lokutan aiki a Sweden

Kotu ta bawa musulmi damar zuwa Sallah a lokutan aiki a Sweden

- Kotu a kasar Sweden ta soke wani doka a garin Malmo na hana musulmi yin Sallah a wurin aiki

- Kotun ta ce kundin tsarin mulkin Sweden ya bawa Kowa iznin ƴin addininsa ba tare da tsangwama ba

- Mahukunta a birnin sun bawa kotu uzurinsu amma kotun ta yi watsi da shi amma a yanzu babu tabbas ko za su daukaka kara

Kotu ta bawa musulmi damar zuwa Sallah a lokutan aiki
Kotu ta bawa musulmi damar zuwa Sallah a lokutan aiki. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya

Wata kotu da ke Malmo a kasar Sweden ta yanke hukuncin cewa musulmi suna da ikon su rika tafiya suyi salla a lokacin da suke wurin aiki.

Hukuncin ya ce dole masu kamfanoni su rika barin ma'aikatansu Musulmi su rika yin sallolinsu biyar a lokacin da suke wurin aiki.

Kotun da ke Malmo ta soke hukuncin da Majalisar Birnin Bromoll da ke kudancin kasar ta yi na hana Sallah a lokacin aiki tun shekarar da ta gabata.

KU KARANTA: Ashariyar da wasu aku 5 ke yi wa mutane a gidan zoo yasa dole an raba su (Hotuna)

An kafa dokar ne a kan dukkan addinai amma ta fi shafan musulmi da ke sallah sau biyar a rana.

Dukkan shugabannin ƙananan hukumomi na Democrats da Kiristoci na Sweden duk sun amince da dokar.

A shekarar 2019, wani mazaunin garin ya koka kan dokar inda aka tura shi kotu.

A cewar hukuncin kotun, dokar da jihar ta kafa na hana musulmi sallah a wurin aiki ta saɓa wa kudin tsarin mulki na Sweden da ya bawa Kowa ikon yin addininsa.

Kotun ta yi watsi da dukkan uzurin da hukumomin jihar suka gabatar a yanzu ba a sani ba ko za su hakura.

A wani rahoton,Yan sanda a Enugu sun kama wani mutum da ya shiga wani wurin bauta ya kama abin bautar da ya ce ya hana mutanen garin cigaba, ya yi sanadin tabarbarewar kasuwanci tare da hana 'yan mata samun mazan aure.

Mutumin mai matsakaicin shekaru, Nnajiofor Donatus ya ce wahayi aka masa ya tafi ya cire abin bautar daga inda ya ke.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel