Adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a dukkan jihohi 36 da Abuja(Jerinsu)
Bayan watanni bakwai da bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu dukkan jihohi Najeriya 36 da kuma babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.
Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ke fitarwa kulli yaumin.
A yayin da cutar ta fara nuna alamun karewa, har yanzu jihar Legas ce ke jan ragama ta yawan masu cutar inda ta harbi mutum 19, 542.
Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 59,001, sai kuma mutum 50,542 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 1112 suka riga mu gidan gaskiya.

Source: Twitter
DUBA NAN: Sai da aka gargadi Zulum kada ya tafi Baga amma yayi kunnen jaki - Tsohon dirakta a DSS
Ga jerin adadin mutanen da suka rage masu dauke da kwayoyin cutar a kowace daya daga cikin jihohi 35 na Najeriya da cutar ta bulla:
Legas - 19,542
Abuja - 5,720
Filato - 3,451
Oyo - 3,267
Edo - 2,628
Ribas - 2,453
Kaduna - 2,426
Ogun - 1,858
Delta - 1,802
Kano - 1,738
Ondo - 1,631
Enugu - 1,289
Ebonyi - 1,042
Kwara - 1,036
Abia - 895
KARANTA NAN: Shugaban Amurka Donald Trump da matarsa sun kamu da cutar korona
Gombe - 883
Katsina - 864
Osun - 842
Borno - 745
Bauchi - 699
Imo - 572
Benuwe - 481
Nasarawa - 452
Bayelsa - 399
Jigawa - 325
Sakkwato - 162
Neja - 259
Akwa Ibom - 293
Adamawa - 248
Kebbi - 93
Zamfara - 78
Anambra - 7
Yobe - 76
Ekiti - 321
Taraba - 102
Kogi - 5,
Cross River - 87
A bangare guda, Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 153 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Alhamis 01 ga watan Oktoba, shekarar 2020.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng