Sai da aka gargadi Zulum kada ya tafi Baga amma yayi kunnen jaki - Tsohon dirakta a DSS

Sai da aka gargadi Zulum kada ya tafi Baga amma yayi kunnen jaki - Tsohon dirakta a DSS

- Tsohon mataimakin dirakta a hukumar tsaron farin kaya ya tofa albarkacin bakinsa kan harin da aka kaiwa gwamna Zulum

- Ya bayyana cewa akwai ka'idojin da ake bi kafin bari wani babba yayi tafiya amma an ki sauraron jami'an tsaro

- Akalla mutane 30 sun rasa rayukansu a harin, wanda ya hada da Sojoji da yan sanda

Wani tsohon mataimakin dirakta a hukumar DSS, Dennis Amakri ya yi tsokaci kan hare-haren da aka rika kaiwa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, kwanakin nan.

Yayin jawabi a shirin Channeks TV na murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun yanci ranar Alhamis, Amakiri ya ce sai da aka gargadi Zulum kan tafiyan nan.

"Sai da aka baiwa gwamnan labarin cewa akwai matsala a hanyar, amma yayi tafiyarsa,:" yace.

"Kuma a matsayinsa na jagoran al'umma, ya fita. An kai masa hari sau biyu. Ina kyautata zaton ba zai sake zuwa ba saboda akalla ana fada mai ya rika kiyaye kansa."

Tsohon dirakta a hukumar ta DSS ya ce akwai ka'idojin da ake bi kafin manyan mutane su fita zuwa wurare.

Ya ce idan ba'a bi wadannan ka'idoji ba, rayuwar shugabanni na iya shiga cikin hadari, musamman yadda mutane ke sukan jami'an tsaro.

KARANTA WANNAN: Jerin adadin: Sabbin mutane 153 sun kamu cutar Coronavirus yau

Sai da aka gargadi Zulum kada ya tafi Baga amma yayi kunnen jaki - Tsohon dirakta a DSS
Credit: @channelstV
Asali: Twitter

DUBA NAN: Zan iya kwato $10bn na fansho daga barayin gwamnati cikin wata 1 kacal - Maina ga Buhari

A ranar 25 ga Satumba, an budewa tawagar motocin ma'aikatan gwamnatin jihar Borno wuta kusa da garin Munguno inda akalla jami'an tsaro 11 suka rasa rayukansu.

Yan ta'addan Boko Haram ne suka bude musu wuta ranar Juma'a yayinda suke hanyarsu ta zuwa Baga, inda gwamnan ke shirin mayar da yan sansanin gudun hijra.

Kwanaki biyu bayan harin, gwamnan ya sake fuskantar wata sabuwar harin a hanyar Baga-Monguno.

A bangare guda, Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnoni da gwamnoni 'yan uwansa sun jawa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum kunne akan ya dinga tsananta tsaro musamman idan zai je wurare masu hadarin gaske, amma sai yace "ya batun mutane na na jihar Borno? Me zai faru dasu?" A wannan halin tashin hankalin dake Borno.

Fayemi yayi wannan maganar ne ranar Laraba yayin da ya jagoranci tafiya tare da gwamnan Sokoto, Tambuwa, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, da kuma Simon Lalong na jihar Plateau, zuwa jihar Borno don jajantawa Zulum akan harin da 'yan ta'adda suka kai wa tawagarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel