Jerin adadin: Sabbin mutane 153 sun kamu cutar Coronavirus yau

Jerin adadin: Sabbin mutane 153 sun kamu cutar Coronavirus yau

Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 153 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Alhamis 01 ga watan Oktoba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 153 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-81

Rivers-21

FCT-11

Ogun-8

Kaduna-7

Oyo-6

Akwa Ibom-5

Osun-3

Katsina-3

Edo-2

Ebonyi-2

Nasarawa-2

Plateau-1

Kano-1

Jimillan wadanda suka kamu: 59,001

Jimillan wadanda aka sallama: 50,452

Adadin wadanda suka yi wafati: 1,112

KARANTA WANNAN: Dan majalisar wakilai ya fasa kwai, ya bayyana kudin albashin da ake biyansu

DUBA NAN: Mahaifiya ta tozarta diyarta bayan kama ta da tayi a dakin otal da namiji (Bidiyo)

A wani labarin mai tashe, Tsohon shugaban kwamitin gyara harkan fansho, Abdulrashid Maina, ya bayyana cewa zai iya kwato kudaden fanshon Najeriya da aka wawura akalla dala bilyan goma cikin wata daya idan shugaba Muhammadu Buhari ya bashi dama.

Maina ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Aliyu Musa, a jihar Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel