Shugaban Amurka Donald Trump da matarsa sun kamu da cutar korona

Shugaban Amurka Donald Trump da matarsa sun kamu da cutar korona

- Shugaban kasar Amurka Donald Trump da mai dakinsa Melania sun kmau da cutar korona

- Shugaba Trump ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a 2 ga watan Oktoban 2020

- Shugaban ya kuma ce shi da mai dakinsa za su killace kansu kuma za su ci galaba kan cutar tare

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da matarsa Melani sun kamu da COVID 19 da aka fi sani da korona kimanin kwanaki 31 kafin zaben shugaban kasa na shekarar 2020 a kasar.

Shugaban kasar ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter bayan daya daga cikin hadimansa Hope Hicks ya kamu da cutar tunda farko.

"A daren yau, ni da @FLOTUS mun kamu da COVID 19. Za mu killace kanmu ba tare da bata lokaci ba. Za mu ci gallaba a kan wannan tare!" kamar yadda ya rubuta.

Shugaban Amurka Donald Trump da matarsa sun kamu da cutar korona
Shugaban Amurka Donald Trump da matarsa sun kamu da cutar korona. Hoto: Thestatesman
Source: UGC

DUBA WANNAN: 'Ka gayyato sojojin Chadi su taya mu yaki da Boko Haram' - Zulum ya roki Buhari

Duba da cewa shugaban na Amurka shekarunsa 74 akwai yiwuwar cutar na iya galabaitar da shi duba da cewa ta fi yi wa mutane masu yawan shekaru illa.

Amma likitan shugaban kasar ya ce Trump da matarsa ba su nuna alamun cutar.

A baya an ruwaito cewa hadiman Trump, Hope Hicks ta kamu da cutar bayan wani tafiya da suka dawo daga tafiya a jirgin sama tare.

A wani labarin kun ji cewa, Lawan Inuwa, dan majalisar Jam'iyyar PDP guda daya tak a majalisar jihar Yobe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya tarbe shi a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu a ranar Laraba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Inuwa dan asalin karamar hukumar Nguru ne kuma yana wakiltar mazabar Nguru ta tsakiya ne a Majalisar Jihar ta Yobe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel