Zan iya kwato $10bn na fansho daga barayin gwamnati cikin wata 1 kacal - Maina ga Buhari

Zan iya kwato $10bn na fansho daga barayin gwamnati cikin wata 1 kacal - Maina ga Buhari

- Watanni bayan samun beli, AbdlRashid Maina ya mikawa shugaba Buhari wata bukata

- EFCC ta gurfanar da Maina a kotu da almundahanan makudan biliyoyin yan fansho

- Ya gudu daga Najeriya tun 2010 amma ya dawo a boye kuma hukumar DSS ta damkeshi a Abuja

Tsohon shugaban kwamitin gyara harkan fansho, Abdulrashid Maina, ya bayyana cewa zai iya kwato kudaden fanshon Najeriya da aka wawura akalla dala bilyan goma cikin wata daya idan shugaba Muhammadu Buhari ya bashi dama.

Maina ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Aliyu Musa, a jihar Kaduna.

A cewarsa, irin wannan kudin zai taimaka wajen gyaran abubuwa, biyan kudin tallafin mai, da kuma yaye matsalar wutan lantarki.

Jawabin yace: "Maina ya bayyana cewa shirye yake da fara kwato kudaden amma shugaba Buhari kadai zai ba, saboda yana tsoron wasu zasu iya sake sace kudin idan ba'a kiyaye ba."

"Maina ya taimakawa gwamnatoci da dama, musamman gwamnatin tsohon shugaban kasa Jonathan inda ya kwato N1.6trillion kuma ya kwatowa gwamnatin Buhari N1.3trillion da dukiyoyi da dama,"

DUBA NAN: Hankali ba zai dauka ba ace Saudi ta fi Najeriya arahar man fetur - Buhari:

Zan iya kwato $10bn na fanshi daga basrayin gwamnati cikin wata 1 kacal - Maina ga Buhari
Maina ga Buhari
Source: Facebook

KU KARANTA: Dan majalisar wakilai ya fasa kwai, ya bayyana kudin albashin da ake biyansu

Za ku tuna cewa wani jami'in hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ya bayyana yadda suka gano asusun banki da dumbin kadarori da sunan Faisal, dan Abdulrashid Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran harkar fansho.

Jami'in na EFCC mai suna Mohammed Goje ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da shaida a gaban wata kotun Abuja a cigaba da sauraron karar Faisal.

A cewar jami'in, a shekarar 2010 ne aka kafa wata tawagar jami'an EFCC domin gudanar da bincike a kan asusun 'yan fansho a ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya da rundunar 'yan sanda.

Yace: "Bincikenmu ya gano yadda Maina ya karkatar da kudaden 'yan fansho zuwa wasu asusun kamfanoni da sunan kwangila. Mun bi diddigin takardun kamfanonin har zuwa ofishin hukumar rijistar masana'antu (CAC), sannan mun bi sunayen masu kamfanin da darektocinsu domin sanin su waye su."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel