Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya

Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya

- A yau Alhamis 1 ga watan Oktoba ne Najeriya ta yi bikin zagayowar ranar samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka

- A halin yanzu Najeriya ta cika shekaru 60 da samun ƴancin kai kuma shekaru 21 da dawowa mulkin demokradiyya

- An gudanar da bukukuwa da dama a ƙasar duk da cewa an takaita bukukuwan saboda annobar korona

A lokacin da Najeriya ke bikin zagayowar ranar samun ƴancin ta, Nduka Orijinmo na BBC ya zaɓo hotuna shida daga cikin kowanne shekara goma da ya ƙunshi muhimman abubuwan da suka faru a tsawon shekaru 60 da samun ƴancin Najeriya.

1960s - Kafuwar Giwar Afirka

Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya
Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya. Hoto: @Daily_trust/Nduka Orjinmo
Source: Twitter

Bayan shekaru da dama turawan mulkin mallaka na jan ragamar ƙasar, Sir Tafawa Ɓalewa ya zama shugaban sabuwar gwamnatin haɗin gwiwa ta Najeriya.

Anyi makonni ana bukukuwa a wasu sassan kasar kuma ga wadanda suke Legas a Tafawa Ɓalewa Square da ke Obalande a ranar 1 ga watan Oktoban 1960, ba za su taba mantawa da ranar ba.

"Daf da karfe 12 na dare, sun kashe wutar lantarki sai aka sauke tutar Birtaniya," a cewar Ben Iruemiobe, wani ɗalibi mai shekaru 16 a lokacin a hirar da ya yi da BBC.

"Karfe 12 na dare na yi, sai suke kunna wutan kawai sai ga tutar Najeriya mai Kore-Fari-Kore an hasko ta ta ƙayatar da kowa.

"Bayan hakan, anyi ta kaɗe-kaɗe da raye-raye."

1970s - Ƴakin basasa da ya yi sanadin mutuwar miliyoyin mutane

Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya
Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya. Hoto: @Daily_trust/Nduka Orjinmo
Source: Twitter

Shekaru bakwai bayan samun ƴancin kai kasar ta faɗa cikin yaƙin basasa a lokacin da mutanen kudu ke son kafa Biafra.

Bayan shekaru uku ana tafka yaƙi, ƴan Biafra sun mika wuya sai dai fiye da mutum miliyan biyu sun mutu galibin su mata da yara saboda yunwa.

Wani marubuci ɗan Najeriya mazaunin Amurka, Okey Ndibe da a lokacin yana ɗan yaro ya bayyana yaƙin a matsayin sanadin mummunan tarihi a Najeriya.

Gwamnati ta yi nasarar ganin kasar ba ta rabu ba amma mutane da dama sun rasa ransu.

"Har yanzu kuruwar Biafra na fitinar Najeriya," in ji shi.

KU KARANTA: Na kashe fiye da mutum 50 don sun kasa biyan kudin fansa - Shugaban masu garkuwa

1980s - 'Ghana Must Go!'

Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya
Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya. Hoto: @Daily_trust/Nduka Orjinmo
Source: Twitter

A shekarar 1983 gwamantin Shugaba Shehu Shagari ta bukaci miliyoyin ƴan gudun hijira daga Afirka ta Yamma galibin su ƴan Ghana su bar Najeriya saboda matsin tattalin arziki da ƙasar ta shiga.

A lokacin ne mafi yawancinsu suka riƙa saka kayansu cikin jakunkuna mai launin fari, ja da shudi wadda daga baya aka sa masa suna "Ghana mustGo" domin komawa kasarsu.

Amma a yanzu an fi musu kallon jakunkuna na talakawa duk da cewa gurbatattun ƴan siyasa na amfani da su wurin jigilar kuɗade.

DUBA WANNAN: 'Ka gayyato sojojin Chadi su taya mu yaki da Boko Haram' - Zulum ya roki Buhari

1990s - Soja mun mika wa farar hula mulki

Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya
Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya. Hoto: @Daily_trust/Nduka Orjinmo
Source: Twitter

Bayan shekaru 16 na mulkin soja duk da cewa an samu takaitaccen mulkin farar hula a 1993, Najeriya ta dawo kan turbar demokradiyya.

Janar Abdulsalami Abubakar ya mika mulki ga Olusegun Obasanjo wanda ya lashe zaben 1999.

Akwai abubuwan tarihi da dama a shekaru 1990s da suka hada da soke zaɓen 1993 da gwamnatin soja ta yi, kisar Ken Saro Wiwa da wasu masu fafutikan kare muhalli 8 ta hanyar rataya da kuma mutuwar Janar Sani Abacha.

2000s - 'Ɓaƙar fata ne mu, muna da kyau kuma ana rububi a kan mu'

Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya
Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya. Hoto: @Daily_trust/Nduka Orjinmo
Source: Twitter

A ranar 16 ga watan Nuwamban 2001, wasu ƴan matan a Najeriya sun shiga gasar sarauniyar kyau na duniya.

A ƙarshe ƴar Najeriya mai shekaru 18 mai suna Agbani Darego ta lashe gasar ta zama mace na farko da ta lashe kambun mace mafi kyau a duniya.

Kafin nasarar ta, galibin kasashen duniya ba su yi wa baƙar fata kallon kyawawa.

Daga wannan lokacin ɗaruruwan mata daga Najeriya suka fara tururuwan shiga gasar.

"Yanzu duniya na son waƙoƙin Afirka, suna son rawar Afirka.

'Ɓaƙar fata ne mu, muna da kyau kuma ana rububi a kan mu," a cewar Ben Murray Bruce, tsohon mai shirya gasar mace mafi kyau a Najeriya a hirarsa da BBC.

2010s - Sace ƴan matan Chibok

Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya
Hotuna: Manyan abubuwan tarihi 6 da suka faru a cikin shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya. Hoto: @Daily_trust/Nduka Orjinmo
Source: Twitter

A watan Afrilun 2014, Kungiyar ƴan ta'adda masu iƙirarin musulunci sun sace ƴan mata 276 daga makarantar su da ke Chibok a arewa maso gabashin Najeriya.

Boko Haram sun sace mutane da yawa a baya amma satar ƴan matan Chibok ya ɗauki hankalin kasashen duniya har da laƙabinsa na #BringBackOurGirls.

Bukky Shonibare, ɗaya daga cikin jagoran masu fafutikan ganin gwamnati ta ceto ƴan matan ta ce sace su ya janyo koma bayan ilimi a arewacin Najeriya.

"Yara - maza da mata suna tsoron zuwa makaranta, iyaye sun shiga tsaka mai wuya, ko su ajiye yaransu a gida ko su tura su makaranta su jefa su cikin hatsari.

"Hakan ya janyo koma baya ga nasarorin da aka samu na ƙaƙarin kawo daidaito tsakanin yara maza da mata," in ji ta.

Bayan shekaru shida, har yanzu fiye da ƴan matan 100 ba su dawo gidajen iyayen su ba.

A wani labarin da daban, kun ji cewa L awan Inuwa, dan majalisar Jam'iyyar PDP guda daya tak a majalisar jihar Yobe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya tarbe shi a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu a ranar Laraba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel